Da duminsa: Makarantar Boko mai hawa 3 ta ruguje a jihar Legas

Da duminsa: Makarantar Boko mai hawa 3 ta ruguje a jihar Legas

- A karo na biyu, ginin makaranta ya ruguje a jihar Legas, kudu maso yammacin Najeriya

- An yi sa'a babu dalibai ko Malamai a cikin makaranta

Ginin makarantar Boko mai suna Excel College ya ruguje dake titin ansarudeen, Ile-Epo, Iyana Ejigbo, dake jihar Legas.

Dirakta Janar na hukumar agaji na gaggawa na jihar Legas, LASEMA, Femi Oke-Osanyintolu ya bayyana cewa wani sashen makarantan da ya rufto.

Oke-Osanyintolu ya ce bisa kiraye-kirayen da ya samu, ginin ya rufto ne misalin karfe 8:15 na safe.

"Bayanan da aka tattara daga wasu ma'aikatan makarantar sun nuna cewa tuni ginin ya nuna alamun gajiya kuma makarantar na shirin gyarawa, "yace

"Ginin mai hawa uku na da sassa biyu a hade. Sashen da ya ruguje ya shafi daya sashen sosai saboda ana iya ganin tsagewa a cikin bango da rukunan ginin."

"An yi sa'a babu wanda ke cikin makarantan, babu wanda ya samu rauni kuma babu wanda ya mutu."

Wannan abu ya faru ne yan watanni bayan wani gini mai hawa uku ya rufto a tsibirin Legas inda mutane 3 suka rasa rayukansu, ciki har da yaro.

Hakazalika ranar 17 ga Yulu, wani gini ya rufta kan mutane a Ogudu inda mutane biyu suka mutu.

KU KARANTA: Yadda zabe gwamnan jihar Edo tsakanin Obaseki da Ize-iyamu ke gudana

Kalli hotuna:

Da duminsa: Makarantar Boko mai hawa 4 ta ruguje a jihar Legas
Da duminsa: Makarantar Boko mai hawa 4 ta ruguje a jihar Legas
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel