Mutumin da yake acaba yana biyawa kanshi kudin makaranta ya zama dalibin da yafi kowa sakamako mai kyau

Mutumin da yake acaba yana biyawa kanshi kudin makaranta ya zama dalibin da yafi kowa sakamako mai kyau

- Wani matashi daga jami'ar ilimi ta Winneba, ya dauki nauyin karatun shi ta hanyar yin acaba, inda a karshe ya kammala da sakamako mafi kyau a jami'ar

- Ya zama dalibin da yafi kowa a fannin da yayi karatu a jami'ar

- Saurayin mai suna George yanzu ya yanke shawarar karatun likitanci, inda kuma ya nuna cewa yana matukar son ya samu wanda zai taimaka masa ya cimma wannan buri na shi

George Ameyaw, dalibin jami'ar ilimi ta Winneba (UEW), wanda ya dauki nauyin karatunsa ta hanyar sana'ar acaba, ya kammala karatu da sakamako mafi daraja.

A wata hira da yayi da Legit.ng, matashin saurayin ya bayyana cewa ya fita da sakamako mai kyau (GPA 3.96), wanda yake shine sakamako mafi daraja da aka taba fita da shi a wannan fanni na jami'ar.

Ya fara acaba a lokacin da yake aji biyu a jami'a, kuma a lokacin babu kudi da zai iya daukar nauyin kansa.

Mutumin da yake acaba yana biyawa kanshi kudin makaranta ya zama dalibin da yafi kowa sakamako mai kyau
Mutumin da yake acaba yana biyawa kanshi kudin makaranta | Source: Facebook, Kweku Ameyaw
Source: Facebook

KU KARANTA: Zargin luwadi: Kotu ta bukaci a adana mata makaho a gidan yari

Da yaga cewa babu wata hanya da zai samu kudi, George sai ya nemi taimako daga kamfanin MTN na kasar Ghana, sannan ya tara wasu kudade ya sayi babur ya fara sana'a.

Kamfanin MTN sun taimaka masa ya biya kudin makarantar shi, kudin gida da kuma kudin takardu, amma dole ya sanya ya dinga daukar nauyin kansa kan wasu abubuwa da sana'ar shi ta Okada.

A karshe makarantar da ya kammala a baya da ya zama dalibin da yafi kowa sakamako mai kyau tayi farin ciki sosai.

KU KARANTA: Duk da bakar wahalar dana sha a kasar Libya, har yanzu ina son komawa can

A yanzu haka dai George yana so yayi karatu a fannin likitanci da tiyata, hakan ya sanya yace zai yi farin ciki sosai idan ya samu wanda zai taimaka masa wajen ganin ya cimma wannan buri na shi.

Shi kuwa wani mutumi mai shekaru 36, mai suna Emmanuel Menuwa, ya bayyana cewa yana samun N700 ne a kowacce rana fiye da shekaru 20 da suka gabata a matsayin lebura.

Da yake hira da Legit TV, Emmanuel, wanda yake aiki a Ogbe-Ijoh Jetty dake Warri, cikin jihar Delta, ya ce yana yin wannan aikin karfine saboda bashi da wani abu da zai yi kuma baya so yayi sata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel