Da duminsa: Sabbin mutum 126 sun sake harbuwa da korona a Najeriya

Da duminsa: Sabbin mutum 126 sun sake harbuwa da korona a Najeriya

Alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC), na ranar Laraba, 16 ga watan Satumban 2020, sun bayyana cewa sabbin mutum 126 sun sake harbuwa da cutar korona a Najeriya.

Lagos-27

Plateau-16

Kaduna-9

Abia-7

Gombe-6

Ondo-6

Imo-5

Delta-2

Ekiti-2

Kwara-2

Oyo-2

Bauchi-1

Kano-1

Katsina-1

Ogun-1

Yobe-1

KU KARANTA: 'Yan daba sun kai wa tawagar Gwamnan APC hari, sun ragargaza ababen hawa

Kamar yadda hukumar NCDC ta bayyana, mutum 56,604 ne suka kamu da cutar, an sallami mutum 47,872 daga asibiti bayan warkewar da suka yi, yayin da mutum 1,091 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da cutar.

KU KARANTA: Motocin kudin da ka kwamushe a gidanka ba za su iya siya maka Edo ba - Ikimi ga Tinubu

A wani labari na daban, hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa an sallami mutane 3442 dake fama da cutar Korona a birnin tarayya Abuja, jihar Kwara da wasu jihohin Najeriya a yau kadai.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:30 na daren ranar Laraba 16 ga Satumba, shekarar 2020.

Hukumar ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 126 a fadin Najeriya. Jawabin hukumar yace: "Warakan da muka samu yau mutane 2,967 a birnin tarayya da 103 a jihar Kwara da aka yiwa jinya cikin gida bisa sharrudan da hukumar ta gindaya."

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 126 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

FCT-37, Lagos-27, Plateau-16, Kaduna-9, Abia-7, Gombe-6, Ondo-6, Imo-5, Delta-2, Ekiti-2, Kwara-2, Oyo-2, Bauchi-1, Kano-1, Katsina-1, Ogun-1, Yobe-1.

Kawo yanzu, jimillan mutane 56,604 suka kamu da cutar a Najeriya, yayinda 47,872 suka warke, 1,091 sun mutu sakamakon cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel