Kada ku karya tattalin arzikin Najeriya da korona - Majalisar dattawa

Kada ku karya tattalin arzikin Najeriya da korona - Majalisar dattawa

- Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a kasar nan da su kiyaye kada tattalin arziki ya fada wani hali na daban

- Kwamitin majalisa na kula da sufurin jiragen sama da lafiya ne ya yi wannan kira a kan salon yaki da korona da aka dauka

- Shugaban kwamitin yaki da cutar na fadar shugaban kasa ya ce talauci da karfinsa a Afrika ne yasa cutar ta kasa kamari

Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan da kada su kashe tattalin arzikin Najeriya ta hanyar daukar salon Turawa wurin yaki da annobar korona.

Majalisar dattawan ta yi wannan zancen ne a ranar Talata sakamakon sabon salon yaki da cutar korona da aka dauka.

Sun samu zantawa tsakanin kwamitin majalisar dattawa da ke kula da sufurin jiragen sama da lafiya, da kuma masu ruwa da tsaki a kan yadda cutar korona ta kasa kamari a Najeriya da sauran kasashen Afrika.

Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Smart Adeyemi, ya ce duba da yadda cutar take, ba daidai bane a ce Najeriya na kwaso tsarin yakar cutar daga Turai, Amurka da China.

Amma kuma, shugaban kwamitin yaki da annobar na fadar shugaban kasa, Dr Sani ALiyu, ya tabbatar da cewa talauci yana daya daga cikin manyan makaman da suka yaki cutar.

A yayin kara bayani, Sanata Adeyemi ya ce, "Babu wani abu da ke tare da 'yan Afrika da babu a Turai da Amurka, wanda yasa cutar korona ba za ta iya yi mana mugun illa ba.

"A saboda hakan, akwai wasu matakan da bai dace kasar nan ta dauka ba duba da yanayin tattalin arzikinmu gudun halakarsa baki daya."

KU KARANTA: La-liga: Ali Nuhu ya zama Jakadan kwallon kafa a Arewacin Najeriya

Kada ku karya tattalin arzikin Najeriya da korona - Majalisar dattawa
Kada ku karya tattalin arzikin Najeriya da korona - Majalisar dattawa. Hoto daga Vanguard
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Bene ya rushe a Kano, ya kashe yara 2 'yan gida daya, mutum 8 sun jigata

A wani labari na daban, fitaccen marubuci Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauya salon mulkin Najeriya, ko kuma akwai yuwuwar dukkanmu za mun fada halaka.

Ya tabbatar da cewa, salon Najeriya babu shakka ba zai haifar da da mai ido ba. Soyinka wanda ya sanar da hakan a wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar Talata, ya ja kunne a kan rabe-raben kan da ake samu a kasar nan wanda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi magana a kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel