Masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne - Farouq Adamu Aliyu, babban na kusa da Buhari

Masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne - Farouq Adamu Aliyu, babban na kusa da Buhari

- Alkaluma daga kungiyoyin lissafin duniya sun nuna cewa Najeriya ta fi ko ina yunwa a duniya

- Jihar Jigawa na daya daga cikin jihohi mafi yawa mabarata masu neman abinci

- Tsohon dan majalisar wakilai, Adamu Aliyu, ya ce duk karya ne

Daya daga cikin manyan na kusa da shugaba Muhammadu Buhari kuma tsohon dan majalisar wakilai, Farouq Adamu Aliyu, ya bayyana cewa duk masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne.

Adamu Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin hira da yake a shirin gari ya waye (Sunrise) na tashar Channels.

Dan siyasan yace a jiharsa na Jigawa, babu yunwa kuma hakazalika sauran jihohin Najeriya.

Yayinda aka yi masa tambaya da rahoton dake nuna cewa Najeriya ce cibiyar yunwa a duniya, Adamu Aliyu yace: "Ban tunanin gaskiya ne saboda jihata da sauran jihohin Najeriya mutane basu jin yunwa."

"Karya ce kawai, a kasar nan babu yunwa."

KU KARANTA WANNAN: Ganduje, Yahaya Bello, da Oshiomole na cikin mutanen da Amurka ta haramtawa shiga kasarta

Masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne - Farouq Adamu Aliyu, babban na kusa da Buhari
Masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne - Farouq Adamu Aliyu, babban na kusa da Buhari
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu yanzu: Allah ya yiwa Sarkin Biu, Mai Umar, rasuwa

A bangare guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a karshen mako, ya ce gwamnatinsa bata shirya bude iyakokin kasar ba a yanzu.

Shugaban kasar ya bukaci yan Najeriya da su ci abunda ake shukawa a kasar.

Ya fadin hakan ne da yake amsa tambayoyi a filin Jirgin sama na Sir Ahmadu Bello, Birnin Kebbi a lokacin wani rangadi don ganin irin barnar da ambaliyar ruwa ya yi a jihar Kebbi.

Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin ministan noma, Mohammed Sabo Nanono, ya ce a shirye gwamnatin tarayya take ta ba manoma tallafi domin bunkasa harkar noma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel