Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a Benue, Nasarawa da Taraba

Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a Benue, Nasarawa da Taraba

- Bayan kashe kasurgumin dan ta'adda 'Terwase Gana', sojoji sun kaiwa yaransa farmaki

- Sojoji sun rugurguza mabuyar wasu makiyaya da suke iyakan Benue da Nasarawa

Dakarun Hukumar Sojin Najeriya sun samu nasarar kai hare-hare uku masu muhimmanci kan yan bindiga a jihohin Nasarawa, Benue da Taraba cikin sabon makon nan da aka shiga.

Diraktan yada labaran hedkwatar Soji, Manjo Janar John Enenche, ya ce a ranar Litinin 14 ga Satumba, dakarun Sector 1 sun ragargaji yan bindiga inda aka lalata mabuyarsu kuma aka jikkatasu.

Enenche ya kara da cewa Sojin sun samu labarin wasu yaran halakakken dan bindiga, Terwase Gana, dake Adu, a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Sakamakon haka, dakarun Sector 2 da Sector 4 suka hada kai wajen kai musu farmaki inda suka hallaka yan ta'adda biyu yayinda saura suka arce cikin daji.

Bata kare a nan na, Enenche ya ce Sojojin sun kai farmaki mabuyar "yan bindiga dake Chancangi a karamar hukumar Takum da ke Taraba da garin Sai dake karamar hukumar Katsina ala na jihar Benue."

"An damke Saalu Igbua Terlumun, Benjamin Valentine da Milton Gbegi a garin Sai yayinda aka damke Isaac Hilega aka Bawasa da Godwin Terwase a Chanchanji."

Jaruman sojin sun samu kwato wayoyin salula 16, layu da ganyen wiwi kuma an kaddamar da bincike kansu gabanin mikasu ga hukumar yan sanda, cewar Manjo Janar Eneche.

KU KARANTA NAN: Kada ku sake ku zabi Obaseki, dan kama-karya ne - Tinubu ya yi jawabi na musamman

DUBA NAN: Fasinja 1 ta ji rauni a harin da aka kaiwa jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna

Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a Benue, Nasarawa da Taraba
Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a Benue, Nasarawa da Taraba
Asali: UGC

A bangare guda, Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane na Ƙasa, NAPTIP ta ce ta ceto mutane 135 tare da kama mutum 86 da ake zargin masu safarar mutane ne a Kano daga watan Janairu zuwa yanzu.

Kwamandan hukumar a jihar Kano, Shehu Umar ne ya bayyana hakan yayin hirar da Kamfanin dillancin labarai, NAN, ta yi da shi ranar Talata a Kano.

Ya ce mutane 135 da aka ceto sun kunshi mata 112 da maza 23.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel