Yan sanda sun kama wani da yayi fim din batsa da kayan mabiya wani addinin gargajiya a Ogun

Yan sanda sun kama wani da yayi fim din batsa da kayan mabiya wani addinin gargajiya a Ogun

- Yan sanda a jihar Ogun sun kama wani mutum da ake zargi da yin fim din batsa a wani lambu a jihar Ogun ya kuma watsa a dandalin sada zumunta

- Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya tafi wani karamin lambu ne a jihar ya kuma nadi bidiyon batsan sanye da kaya na wasu mabiya addinin gargajiya

- Yan sanda sun ce za su gudanar da bincike a kan lamarin kana za su gabatar da wanda ake zargin a kotu idan akwai bukatar hakan

Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta damke wani mutum mai suna Tobilola Jolaosho a kan zarginsa da nadar bidiyon batsa a wani karamin lambu da ke Osogbo.

Jolaosho, wanda aka zarge sa da lalata da wata mata wacce ta bayyana tsirara, ya nadi bidiyon a watan Yulin shekarar nan sannan ya wallafa shi a kafafen sada zumuntar zamani.

An kama wani da ya yi fim din batsa a wani lambu a Ogun
An kama wani da ya yi fim din batsa a wani lambu a Ogun
Asali: UGC

A lokacin da The Punch ta tuntubi rundunar 'yan sandan jihar, kakakin rundunar, Yemisi Opalola, ya tabbatar da kamen Jolaosho.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke makusancin Gwamna Yari yana taron sirri da 'yan bindiga a Zamfara

Ta yi bayanin cewa an kama shi sakamakon korafin da wata kungiyar mabiya addinin gargajiya a jihar Osun ta bada. Akwai yiwuwar Jolaosho zai iya haifar da karantsaye na zaman lafiya a yankin.

Kakakin rundunar 'yan sandan ta ce, "Awosunwon da ke Idinleke a Osogbo ya sanar da 'yan sanda cewa ya ga Tobiloba Isaac Jolaosho yana sanye da wasu kayan gargajiya tare da wata mace tsirara suna bidiyon batsa kuma ya watsa a kafafen sada zumuntar."

DUBA WANNAN: Gana ya san zai mutu, ya nada wanda zai gaje shi

Ta kara da cewa, tuni 'yan sanda suka ziyarci inda lamarin ya faru kuma sun bada tabbacin cewa za su yi bincike tare da gurfanar da wanda ake zargin idan bukatar hakan ta tashi.

A wani labarin, kun ji cewa tsawa ta kashe mutum hudu cikin manoma biyar da suka fake a kasan bishiya yayin da ake tafka mamakon ruwan sama a kauyen Kukar-Gesa da ka karamar Katsina ta jihar Katsina.

Malam Musa Danladi, shugaban iyalan ya tabbatar da mutuwar 'ya'yansa biyu da jikansa daya kuma ya danganta hakan da hukuncin Ubangiji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel