Kawunnan ƴan Najeriya sun rabu, ƙasar ta kama hanyar rugujewa: Obasanjo ya sake sukar Buhari

Kawunnan ƴan Najeriya sun rabu, ƙasar ta kama hanyar rugujewa: Obasanjo ya sake sukar Buhari

- Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Najeriya ya sake sukar gwamantin Shugaba Muhammadu Buhari

- Obasanjo ya koka kan yadda rarrabuwar kai ke ƙaruwar a kasar da kuma tsananin talauci

- Tsohon shugaban kasar ya kuma soki yan siyasa da ke batun zaben 2023 a yanzu a maimakon gyaran ƙasa

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya sake sukar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari inda ya ce ƙasar ta kama hanyar lalacewa kuma kawunnan yan kasar sun rabu.

Obasanjo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a wurin wani taron da kungiyoyi masu wakiltan yankunan kasar suka hallarta.

Ba a taɓa samun rarrabuwar kawuna irin ta yanzu ba a Najeriya: Obasanjo ya sake sukar Buhari
Ba a taɓa samun rarrabuwar kawuna irin ta yanzu ba a Najeriya: Obasanjo ya sake sukar Buhari
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Taron da aka yi a ranar Alhamis 10 ga watan Satumba a Abuja ya samu hallarci kungiyoyi kamar Afenifere, Middle Belt Forum, Northern Elders Forum, Ohanaeze Ndigbo da sauran su.

Tsohon shugaban kasar ya ce bai taba ganin rabuwar kai a Najeriya ba kamar wadda aka samu a ƙarƙashin gwamnatin Buhari.

Ya kuma nuna bakin cikinsa a kan yadda Najeriya da zama babban birnin talauci na duniya.

"Na ji dadin yadda kuma kuke bakin cikin halin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a yanzu. A yanzu Najeriya ta kama hanyar rugujewa ga kuma rarrabuwar kai; a fanin tattalin arziki kasar mu kama hanyar zama babban birnin talauci na duniya ga kuma rashin tsaro," kamar yadda Obasanjo ya fadi a wani sashi na jawabinsa.

A cewar tsohon shugaban ƙasar mutane marasa hankali ne kawai za su yi iƙirarin cewa Najeriya ba ta cikin matsala.

KU KARANTA: An kama wani da yayi shekaru 2 yana karbar albashin kwamishina a Niger

Ya kuma soki wasu yan siyasa a ƙasar da tun a yanzu sun fara batun zaben shekarar 2023 a maimakon su mayar da hankali wurin gyaran ƙasa.

"Na yi imanin bai dace a bari Najeriya ta ruguje ba muddin za ayi aiki tare, za a iya cimma hakan ta hanyar tattaunawa a maimakon cacar-baki da rikici. Wanda ba shi da hankali ne kadai zai yi iƙirarin komai na tafiya dai-dai a Najeriya," in ji Obasanjo.

A wani rahoton, kun ji cewa ofishin hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati, EFCC, ta fara bincike a kan wani da ake zargin ɗan damfara ne da aka kama ya ɓoye katim ATM 2,886 da layyukan waya hudu cikin taliyar indomie.

Jami'an hukumar Kwastam ne suka mika wanda ake zargin, Ishaq Abubakar ga hukumar EFCC a ranar Alhamis 10 ga watan Satumban 2020 domin a bincike shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel