Kayayyakin abinci sun yi sauki a kasuwannin Najeriya, in ji Garba Shehu

Kayayyakin abinci sun yi sauki a kasuwannin Najeriya, in ji Garba Shehu

- Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya ce farashin kayan abinci na sauka a Najeriya

- Shehu ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke martani a kan koken da ake yi na tsadar kayan abinci

- Shehu ya bayar da misalan yadda farashin wasu kayan abinci suka yi sauki kamar yadda rahoton majalisar abinci na ƙasa ya nuna

Garba Shehu, Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari ya ce farashin kayayyakin abinci suna sauka a kasuwanni akasin ƙorafin da mafi yawancin mutanen ke yi.

Garba ya yi wannan furucin ne yayin hirar da aka yi da shi a ranar Juma'a 11 ga watan Satumba a Channels TV da ya ke magana a kan umurnin da Buhari ya bawa bankin ƙasa CBN na dena yiwa masu shigo da abinci da kayan noma canjin kuɗi.

Farashin kayayyakin abinci a Najeriya suna sauka - Garba Shehu

Farashin kayayyakin abinci a Najeriya suna sauka - Garba Shehu. Hoto daga LIB
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Wani babban malami a Tsangayar Nazarin tattalin arziki a Jami'ar Abuja, Dakta Ahmed Adamu ya soki matakin da shugaban ya ɗauka.

A cewarsa bai dace Shugaban kasar ya bada wannan umurnin ba a lokacin da aka samu hauhawan farashi kayayyaki a kasar.

"Yanzu za mu riƙa ganin hauhawan farashin kayan abinci a kasar kuma wannan matakin zai ƙara janyo tsadar kayan abinci a lokacin da ƴan Najeriya ke fito wa daga kullen annobar korona," in ji Adamu.

KU KARANTA: An kama wani mutum dauke da katin ATM 2,886 a filin jirgin sama zai tafi Dubai (Hotuna)

Da ya ke yin martani a kan abinda malamin jami'ar ya fadi, Garba ya ce;

"Kuskure ne a ce rufe iyakoki na da alaƙa da tsadar kayan abinci. Sannan cewa farashin kayan abinci ba su sauka na nuna cewa malamin bai da masaniya a kan abubuwan da ke faruwa a kasuwanni saboda munyi taro da majalisar tsaron abinci na ƙasa kuma mun saurari abinda kwararru da suka yi nazarin kasuwanni suka faɗa.

"A safiyar jiya (Alhamis) da ke muke taron, ka tafi ka duɓa alƙalluman kasuwanni. Misali a kasuwannin Kano, Gero da ake sayar wa N24,000 yanzu ya sako zuwa N12,000 zuwa N13,000. Shinkafa kuma da kuɗin ta ya kai N25,000 yanzu ta sako zuwa N20,000. Tsohon masara yanzu N18,000 yayin da sabo kuma N14,000 zuwa N15,000.

"Saboda haka cewa ba a samu canji a farashin kayan abinci ba na nuna cewa mutum bai san abubuwan da ke faruwa a ƙasa ba."

Da ya ke martani kan cewa ba dukkan yan Najeriya ne suka samu sauƙin ba, Garba ya ce;

"Kaman yadda Jamusawa ke cewa, idan kana son sanin yanayin da gari ke ciki to ka buɗe tagar gidan ka. Ina shawartar yan jarida su shiga kasuwanni su tambayi farashin kayan abinci.

"Ban ce farashin komai ya sakko ba amma dai suna sauka. Suna sauka saboda sabbin kayan gona suna shigowa kasuwanni. Za a cigaba da samun saukin idan manoma na kawo kaya kasuwa. A kan samu hakan duk shekara."

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kafa wata kwamiti da za ta cigaba da jan ragamar bunkasa tattalin arzikin ƙasar mai suna Agenda 2050.

Wannan kwamitin za ta ɗora ne a kan tsarin tattalin arziki na vision 2020 da tsohon shugaban kasar Musa Yar'adua ya kaddamar da wasu tsare tsaren.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel