Sabbin yan Najeriya 197 sun kamu da cutar Korona

Sabbin yan Najeriya 197 sun kamu da cutar Korona

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 197 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Alhamis 10 ga Satumba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 197 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Plateau-83

Lagos-48

Kaduna-17

FCT-16

Ogun-11

Katsina-7

Imo-4

Edo-3

Nasarawa-3

Rivers-2

Bayelsa-1

Oyo-1

Osun-1

A bangare guda, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta “kashe kudi N30,540,563,571.09, wanda ya yi daidai 84% na naira biliyan 36.3 na kudaden jama’a da gudunmawar da ta karba domin magance lamarin kororna tsakanin 1 ga watan Afrilun 2020 da 31 ga watan Yulin 2020, kudin da ya yi saura a yanzu naira biliyan 5.9 ne.”

Babban ma’ajin gwamnatin tarayya, Agmed Idris, ya bayyana hakan a yayinda yake amsa bukatar da kungiyoyin Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) da Connected Development (CODE) suka nema mai kwanan wata 10 ga Agustan 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel