Da duminsa: Mun ceto mutane 5 cikin wadanda aka sace a Abuja cikin daren Laraba - Yan sanda

Da duminsa: Mun ceto mutane 5 cikin wadanda aka sace a Abuja cikin daren Laraba - Yan sanda

Hukumar yan sandan Najeriya ta tabbatar da labarin cewa yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutane 10 a garin Tungan Maje, waje-wajen birnin tarayya a Abuja cikin daren Laraba.

Legit ta ruwaito muku cewa Premium Times ta samu labari daga wani mazaunin garin.

A jawabin da ya saki ranar Alhamis, Kakakin hukumar yan sanda a birnin tarayya, DSP Anjuguri Manzah, ya ce jami'an hukumar sun ceto mutane biyar cikin goman da aka sace.

"Hukumar yan sandan FCT na son tabbatarwa al'umma cewa kare rayuka da dukiyoyinsu ne babbar manufarmu kuma zamu cigaba da kawo dabarun da zasu taimaka wajen tsare birnin tarayya." A cewarsa.

KU KARANTA WANNAN: Bayan babban fashewar watan jiya, gobara ta sake kamawa a birnin Beirut, kasar Lebanon (Hotuna da Bidiyo)

Legit ta kawo muku rahoton cewa Yan bindiga sun kai farmaki garin Tungan Maje, waje-wajen birnin tarayya Abuja, inda sukayi awon gaba da mutane da ba'a san yawansu ba har yanzu.

Premium Times ta samu labari daga wani mazaunin garin cewa akalla mutane 20 aka sace bayan dogon lokaci ana harbe-harbe a cikin garin.

Wani mazaunin unguwar da aka sakaye sunansa ya ce sun fara jin harbe-harben bindiga ne misalin karfe 12:15 na dare kuma sai da aka kwashe awa daya ana yi.

Ya ce an galabi yan bangan dake garin.

"Bamu yi bacci ba gaba daya cikin dare. Sai da safen nan yan banga suka fada mana cewa an yi awon gaba da kimanin mutane 20," Yace

Da duminsa: Mun ceto mutane 5 cikin wadanda aka sace a Abuja cikin daren Laraba - Yan sanda
Da duminsa: Mun ceto mutane 5 cikin wadanda aka sace a Abuja cikin daren Laraba - Yan sanda
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sheikh Murtala Sokoto ya ce irinsu Isa Pantami su ka fi dacewa da shugabanci

Wannan harin ya biyo bayan da Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa yan ta'addan Boko Haram na shirin kai farmaki babbar birnin tarayya Abuja, da jihohin da ke makwabtaka.

Gwamnatin ta ce yan ta'addan na shirin kai hari ne wasu wurare na musamman a birnin tarayya kuma tuni sun kafa mabuya guda biyar a Abuja.

A cewar wata takardar da Kontrollan hukumar hana fasa kwabri wato kwastam, H.A Sabo, ya saki ranar 20 ga Agusta, 2020, ya bukaci dukkan hafsoshin su kasance cikin farga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel