Malami ya sanar da abinda zai yi idan aka gayyacesa shaida a gaban kwamitin binciken Magu

Malami ya sanar da abinda zai yi idan aka gayyacesa shaida a gaban kwamitin binciken Magu

Abubakar Malami, antoni janar na tarayya, ya ce da gaggawa zai garzaya bada shaida a kan dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, a gaban kwamitin bincike na fadar shugaban kasa idan an gayyacesa.

Antoni janar na tarayyan yace matukar aka gayyacesa, zai gaggauta zuwa kamar yadda mulkin shugaba Buhari ya horesu da mutunta doka, The Cable ta wallafa.

Kwamitin bincike na fadar shugaban kasa wanda ya samu jagorancin Ayo Salami, wanda ke bincikar Magu a kan zargin rashawa da Malami ya yi a kansa.

Antoni janar ya zargesa da kin aiki da ra'ayin kasar nan tare da dokokin gwamnatin nan, ta yadda ake waddaka tare da rashin gaskiya wurin ajiyar kadarorin da aka karbo daga mahandama.

KU KARANTA: Yadda jami'ai suka yi wa matashiya fyade a motar kaita asbiti bayan kamuwa da korona

Malami ya sanar da abinda zai yi idan aka gayyacesa shaida a gaban kwamitin binciken Magu
Malami ya sanar da abinda zai yi idan aka gayyacesa shaida a gaban kwamitin binciken Magu. Hoto daga The Cable
Source: Twitter

KU KARANTA: Buhari: Abinda na sanar da Trump a yayin da ya zargeni da kashe Kiristoci

A makon da ya gabata, lauyan Magu, ya rubuta wasika ga kwamitin bincike na fadar shugaban kasar a kan su kira Malami domin bada shaida a kan zargin da yake yi wa Magu.

A yayin zantawa da wani shirin Arise TV a ranar Laraba, antoni janar ya ce babu shakka zai je idan kwamitin ya yi kiransa.

"Idan har kwamitin Ayo Salami ta gayyaci Abubakar Malami domin bada shaida ko tuhuma a kan lamarin, babu shakka Abubakar Malami zai amsa gayyatar da dukkan kokarinsa," yace.

Ya kara da cewa, ya amsa gayyata ire-iren wannan kala-kala, domin haka ta kwamitin Ayo Salami ba za ta zama wata daban ba.

A wani labari na daban, Atoni janar na tarayya, Abubakar Malami, ya ce binciken Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu da ake yi ya kara nuna nagartar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Malami ya fadi hakan a wani shirin NTA a daren ranar Juma’a, da yake mayar da martani ga tambayoyin mai gudanar da shirin, Cyril Stober.

AGF din ya bayyana cewa binciken dakataccen Shugaban na EFCC ya nuna cewa babu wanda ya fi karfin doka, Jaridar The Punch ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel