Bai kamata a kama yan bindigan ba ballanta, sun zi mika wuya ne- Gwamnan Benue Ortom

Bai kamata a kama yan bindigan ba ballanta, sun zi mika wuya ne- Gwamnan Benue Ortom

Dakarun Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka dan bindigan da aka dade ana nema ruwa a jallo, Terwase Akwaza, wanda aka fi sani da 'Gana' tare da yaransa.

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana haka ga manema labarai a daren Talata yayinda yake hira da manema labarai bayan tarban yan bindigan daga karamar hukumar Logo, da Katsina Ala

Ortom ya ce Gana da yaransa na hanyarsu wajen zuwa cikin gari domin mika wuya ne lokacin da Sojoji suka tareshi a shataletalen Yandev dake karamar hukumar Gboko, Punch ta ruwaito.

Ortom yace: "Misalin karfe 4 na yamma da muke sauraron zuwan tubabbun yan bindigan na samu kiran waya cewa Sojoji sun damkesu kusa da shataletalen Yandev a Gboko.

"Da yawa cikin tubabbun yan bindigan na da makamai da suke shirin mika mana."

"Jami'an tsaron na sane da shirin yafewa yan bindiga, saboda haka ban san dalilin da yasa zasu kamasu ba."

"Ina samun labarin haka na tuntubi kwamandan Operation Whirl Stroke, Janar Yekini, kuma ya fada min suna artabu lokacin amma zai kirani daga baya; saboda haka har yanzu ina sauraron sa."

"Mutanen nan sun shirya ajiye makamansu ne, zamu kare su,"

Gwamnan yace an kai yan bindiga 46 cikin 172 da aka kama gidan gwamnati kuma ya yi alkawarin za'a sake su.

KU KARANTA WANNAN: An dakatar da Likitoci biyu kan mutuwar wata jaririya a Asibiti

Bai kamata a kama dan bindiga, Gana, ba ballanta kashe shi - Gwamnan Benue Ortom
Bai kamata a kama dan bindiga, Gana, ba ballanta kashe shi - Gwamnan Benue Ortom
Asali: Facebook

Dubun Shahrarren dan bindigan da aka dade ana nema ruwa a jallo, Terwase Agwaza Gana, ya cika hannun jami'an Sojin 'Special forces' a jihar Benue.

Kwamandan 4 Special Forces Command, Doma, jihar Nasarawa, Maj. -Gen. Moundhey Ali, ya bayyanawa manema labarai ranar Laraba cewa an kashe Gana ne a hanyar Gbese-Gboko-Makurdi bayan musayar wuta.

Yace, "Misalin karfe 12:00 na ranar Talata, mun samu labarin shahrarren dan bindiga Terwase Akwaza Agbadu wanda aka fi sani da Gana na hanyar Gbese-Gboko-Makurdi.

"Dakarun rundunar Operation ‘Ayem Akpatuma III’ suka bazama tare hanyar."

"Misalin karfe 13:00, an yi musayar wuta tsakanin Soji da Gana inda aka kasheshi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel