An dakatar da Likitoci biyu kan mutuwar wata jaririya a Asibiti

An dakatar da Likitoci biyu kan mutuwar wata jaririya a Asibiti

Kotun ladabtar da Likitoci a Najeriya ta kama Likitoci biyu - Iyoha Joseph da Mukaila Oyewumi Oladipo - da laifin sakaci wajen kula da wata jaririya mai suna, Oluwole Johnson Peace, wacce ta mutu hannunsu.

A jerin tuhume-tuhume bakwai da aka yiwa Likitocin, kotun ta bayyana cewa Likitocin sun nuna rashin kwarewarsu wajen kula da jaririyar mai watanni uku a duniya ta hanyar rashin bada magungunan da ya kamatan The Nation ta ruwaito.

Yayin yanke hukunci kan lamari, shugaban kotun, Farfesa Abba Hassan Waziri, ya ce Dr Joseph, wanda aka kama da laifuka uku, bai nuna kwarewa ba inda ya baiwa yar wata uku a duniya Chloroquine, Fansidar da wasu magunguna.

Shugaban ya ce Likitan ya karawa jaririyar magungunan zazzabin cizon sauro duk da cewa an riga da bata alluran Arthemether.

A bangare dayan Likitan, Mukaila Oyewumi Oladipo, an kama shi da laifuka biyu na bata lokaci kimanin minti 30 wajen rubuce-rubuce maimakon aikin gaggawa kan jaririyar lokacin da ya ga tana cikin halin rai hannun Allah.

KARANTA WANNAN: Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindigan jihar Benue, Terwase Gana

An dakatar da Likitoci biyu kan mutuwar wata jaririya a Asibiti
An dakatar da Likitoci biyu kan mutuwar wata jaririya a Asibiti
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sulhu alkhairi ne: Yan bindigan Sokoto sun mika wuya, su sake mutane 8 da suka sace

A bangare guda, Kungiyar NARD ta likitoci ta bayyana cewa mambobinta sun soma aiki ne a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, 2020.

Likitocin asibitocin kasar sun tafi yajin aiki a sakamakon gaza zama da shugabanninsu da gwamnatin tarayya ta yi a ‘yan kwanakin bayan nan.

Bayan tafiya yajin aiki, kungiyar NARD ta yi kira ga sauran kungiyoyin ma’aikatan asibiti ta mara mata baya a wannan gwagwarmaya da ta ke yi.

Kungiyar NARD ta bukaci ungonzoma da masu bada magani da sauran likitoci su amsa wannan kira domin ganin an kara yawan alawus din da ake ba su

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa kungiyar NARD ta na fafatukar ganin an karawa Malamai alawus ne a sakamakon hadarin da su ke fuskanta a bakin aiki.

A Najeriya, N5, 000 kacal ne alawus din da gwamnati ta warewa likitoci saboda yiwuwar fuskantar hadari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel