Bidiyo: Amarya ta fasa auren mijinta a lokacin da aka tafi wurin daurin aure

Bidiyo: Amarya ta fasa auren mijinta a lokacin da aka tafi wurin daurin aure

Bidiyon wata amarya sanye da kayan amare ya bazu a dandalin sada zumunta inda aka gano ta tana ihu tana cewa ta fasa auren.

A cikin bidiyon, an haska matar sanye da kayan amare tana ihun cewa ta fasa yin auren.

Baƙi da suka hallarci ɗaurin auren sun yi ƙoƙarin ji ta bakin ta domin sanin dalilin da yasa ta canja ra'ayinta a ranar ɗaurin auren amma bata basu amsa ba.

Bidiyo: Amarya ta fasa auren mijinta a lokacin da ake shagalin biki
Bidiyo: Amarya ta fasa auren mijinta a lokacin da ake shagalin biki. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wata mata mai shekaru 31 ta fada dam ta mutu yayin daukan hotuna

Bidiyon ya nuna matar tana gudu a kan titin sanye da farin kayan amare a yayin da mutane ke ƙoƙarin su dakatar da ita.

Ga dai bidiyon a ƙasa:

A wani labarin daban, kun ji cewa wata mata ta zame ta faɗa cikin dam a lokacin da ta ke ɗaukan hotuna yayin wata liyafar cin abinci na masoya da aka yi a Chepkiit Waterfalls da ke yankin Nandi.

Ruwa ya yi awon gaba da Dorcas Jepkemoi Chumba mai shekaru 31 a ranar Lahadi yayin da saurayinta Banjamin Kazungu ke amfani da wayan ta yana ɗaukan ta hoto.

Iyalan Miss Chumba da suka fito daga kauyen Kapchorwa a Keiyo ta Kudu sun tare a Chepkiit Waterfalls tun ranar Lahadi da nufin za a gano gawarta.

Masunta a yankin da ke neman gawar ta ba suyi nasara ba a lokacin da ake haɗa wannan rahoton kamar yadda da Nation ta ruwaito.

Ɗan uwan ta Victor Kiptoo ya roki gwamnatin Uasin Gishu da Nandi su taimake su wurin gano gawar ta.

"Abin ya faru kuma mun rungumi ƙaddara, roƙo kawai muke yi a taimake mu a gano gawar ta," in ji shi.

KU KARANTA: Soja ya buɗe wa ƙananan yara wuta a kusa da fadar shehun Borno, ya kashe ɗaya

Shugaban ƴan sanda na yankin Nandi, Samson Ole Kina ya ce ambaliyar ruwa ce ke kawo cikas wurin gano gawar.

Ya bukaci iyalan wacce ta rasun su ƙara haƙuri yayin da jami'an da ke aikin za su cigaba da nazarin lamarin.

"Dam ɗin ya zama wuri mai hatsari musamman a lokacin damina, ana shawartar mutane su dena zuwa wurin don tsare lafiyar su," in ji shi.

Ƙoƙarin da Mista Kazungu ya yi na ceto masoyiyarsa bai cimma nasara ba duba da irin karfin ruwa wadda dole haka ya yi ta kallon sahibarsa ruwa na tafiya da ita.

"Na yi ƙoƙarin ceto ta amma banyi nasara ba duba da cewa dam ɗin ya cika maƙil," a cewarsa bayan afkuwar mummunan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel