Yanzu yanzu: Sabbin yan Najeriya 155 sun kamu da cutar Korona

Yanzu yanzu: Sabbin yan Najeriya 155 sun kamu da cutar Korona

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 155 a fadin Najeriya.

Yanzu jihar Plateau ya shiga jerin manyan jihohi biyar masu mafi yawan masu cutar a najeriya

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Litinin 7 ga Satumba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 125 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-42

Plateau-25

Rivers-16

Ebonyi-10

Abia-9

Ogun-9

FCT-9

Osun-7

Katsina-6

Kaduna-6

Ekiti-4

Taraba-4

Edo-3

Anambra-2

Akwa Ibom-2

Kano-1

55,160 sun kamu

43,231 aka sallama

1,061 sun mutu

KU KARANTA: Ya zama dole a dakatar da wannan haukan – Sultan ya yi magana kan kashe-kashen kudancin Kaduna

A bangare guda, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta “kashe kudi N30,540,563,571.09, wanda ya yi daidai 84% na naira biliyan 36.3 na kudaden jama’a da gudunmawar da ta karba domin magance lamarin kororna tsakanin 1 ga watan Afrilun 2020 da 31 ga watan Yulin 2020, kudin da ya yi saura a yanzu naira biliyan 5.9 ne.”

Babban ma’ajin gwamnatin tarayya, Agmed Idris, ya bayyana hakan a yayinda yake amsa bukatar da kungiyoyin Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) da Connected Development (CODE) suka nema mai kwanan wata 10 ga Agustan 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel