An kashe 2, an raunata wasu 2 a harin da IPOB ta kai wa mutanen Hausawa a Ribas

An kashe 2, an raunata wasu 2 a harin da IPOB ta kai wa mutanen Hausawa a Ribas

Akalla ba a kasara, mutane biyu ake zargin sun mutu a a garin Oyigbo, jihar Ribas bayan da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne su ka kai masu hari.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, 2020, cewa an hallaka wadannan Hausawa ne a inda su ke zama a karamar hukumar Oyigbo.

Wani wanda abin ya auku a gabansa, ya ce miyagun ‘yan kungiyar IPOB sun aukawa wadannan Bayin Allah ne a ranakun Asabar da Lahadi da su ka gabata.

Bayan mutum biyu da aka kashe, ana zargin an yi wa akalla wasu mutum biyu mummunan rauni.

Ya ce: “Abin da ya yi kama da harin da aka tsara ya fara ne ranar Asabar, ya kai zuwa Lahadi. Wasu matasa da ake tunanin ‘ya ‘yan IPOB ne sun kai wa ‘Yan kabilar Hausa farmaki, su ka auka masa da manyan makamai.”

Wannan shaida ya kara da cewa: “An ce an kashe mutum biyu a harin, yayin da wasu biyu su ka gamu da rauni sosai.”

KU KARANTA: Kotu ta yankewa mutane 9 hukuncin kisa a Kano a shekarar 2020

An kashe 2, an raunata wasu 2 a harin da IPOB ta kai wa mutanen Hausawa a Ribas
Gwamna Nyesom Wike na Ribas
Asali: UGC

Mai magana da yawun bakin mutanen Arewa da ke zaune a Ribas, Alhaji Musa Saidu, ya tabbatarwa ‘yan jarida da aukuwar wannan labari maras dadi.

Alhaji Musa Saidu ya ce wasu tsageru da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne sun kai wa mutanensu hari a karamar hukumar Oyigbo, har kuma aka rasa rayuka.

Kakakin kabilun Arewan ya ce a ranakun Asabar da Lahadi ne wadannan matasa su ka shiga yankin Oyigbo inda ake da tarin Hausa, su na dauke da makamai.

Alhaji Saidu ya ce an kashe Hausawa biyu da su ke kananan kasuwanci a garin, sannan an bar wasu biyu da munanan raunuka kamar yadda wata majiya ta tabbatar.

Mutanen Arewan sun yi kira ga jami’an tsaro su binciki wannan ta’adi. Har yanzu ba a san abin da ya kawo wannan kisa ba domin ba a iya jin ta bakin ‘yan sandan Ribas ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel