Idan kana tsoron mutuwa a shekaru 70, to ka binciki imaninka - Malamin coci

Idan kana tsoron mutuwa a shekaru 70, to ka binciki imaninka - Malamin coci

- Fasto Adeboye ya yi addu’a kan korona a yayin addu’ar Lahadin farko na cocin RCCG

- Malamin ya ce Allah ya adana mutanensa har watan Satumba sannan zai kare su daga cutar

- An bukaci jama’an taron da su ci gaba da gode ma Allah kan ayyukan ban sha’awa nasa

Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye ya ce duk mutumin da ya fi shekaru 70 kuma yake tsoron mutuwa akwai bukatar ya binciki imaninsa.

Da yake wa’azi a lokacin taron godiya na sabuwar shekarar RCCG wanda aka gudanar a hedkwatarta da ke Lagas, malamin ya bayyana cewa shawarar da gwamnati ta bayar na hana tsoffi zuwa coci abu ne mai kyau.

Sai dai Adeboye, ya yi wata tunatarwa a kan mutuwa, cewa sakon Ubangiji zai isa a kan duk wani mai rai, NAN ya ruwaito.

Idan kana tsoron mutuwa a shekaru 70, to ka binciki imaninka - Malamin coci
Idan kana tsoron mutuwa a shekaru 70, to ka binciki imaninka - Malamin coci Hoto: @PastorEAAdeboye
Asali: Twitter

“Saboda annobar Coronavirus, an shawarci tsoffi da su zauna a gida sannan kada su zo coci wanda hakan shawara ce mai kyau.

“Amma idan ka fi shekaru 70 sannan kuma kana tsoron mutuwa, toh lallai ka binciki imaninka,” in ji malamin.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama dattijo dan shekaru 50 da ya yi wa karamar yarinya fyade a masallaci

Shugaban na RCCG ya bayyana cewa Allah zai halaka coronavirus kuma babu annobar da za ta kusanci ‘ya’yansa.

“Allah zai bamu cikakken nasara a kan kowace cuta. Allan da ya barmu har muka ga watan Satumba zai barmu mu ga sabuwar shekara,” ya yi addu’a.

Malamin ya bukaci taron jama’an da kada su daina yi wa Allah godiya a kan dukkanin abubuwan da Ya yi.

A ranar Talata, 25 ga watan Agusta, RCCG ta sanar da cewa za ta gudanar da taro a watan Satumban 2020 ta yanar gizo.

A cewar cocin, za ta ci gaba da tsarinta na gudanar da tarukan addu’a ta yanar gizo.

Legit.ng ta rahoto cewa a wata sanarwa daga mahukuntan sun ce Fasto Adeboye ne ya yanke hukuncin domin kada ya jefa kowa cikin hatsari idan suka fito daga gidajensu don halartan taro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel