Yan bindiga sun budewa motoci wuta a hanyar Kaduna zuwa Abuja, Sojoji sun kawar da su

Yan bindiga sun budewa motoci wuta a hanyar Kaduna zuwa Abuja, Sojoji sun kawar da su

Jami'an Sojoji da yan sanda sun kawar da wasu yan bindiga da suka budewa matafiya wuta a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Juma'a, 4 ga watan Satumba, 2020.

Daily Trust ta tattaro cewa babu wanda ya mutu amma wasu matafiya da jami'an tsaro sun jikkata kuma ana kula da su.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce jami'an tsaro sun samu nasarar kawar da yan bindigan.

Sun bude wutan ne kusa da kamfanin abincin kaji na Olam.

Kwamishanan harkokin tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a wajen ya ce an fara jinyar wadanda suka jikkata a asibitin kamfanin Olan kafin aka garzaya da shi babban asibiti.

"Jami'an tsaron kasa da sama yanzu haka na bibiyan sauran yan bindigan cikin daji," Yace.

Aruwan ya ce an sanar da gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i kan abinda ke faruwa kuma ya jinjinawa jami'an tsaro bisa jajircewan da suka nuna wajen kawar da yan bindigan.

"Hukumomin tsaro zasu bada cikakken bayani kan abinda ya faru a wajen gaba daya," Ya kara

Yan bindiga sun budewa motoci wuta a hanyar Kaduna zuwa Abuja, Sojoji sun kawar da su
Yan bindiga sun budewa motoci wuta a hanyar Kaduna zuwa Abuja, Sojoji sun kawar da su
Asali: UGC

A wani labari mai alaka, Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce dakarun ta na Operation Thunder Strike sun kashe ƴan bindiga masu yawa a harin da ta kai sansaninsu da ke dajin Kuduru da Kuyambana a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ta musamman, Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da hakan ta shafin rundunar na Twitter a ranar Juma'a a Abuja.

Enenche ya ce sojojin sun samu sahihan bayanan sirri da ke nuna yan ta'addan na amfani da wuraren don shirya kai hari kafin aka far musu.

Ya ce an kai harin a maɓuyar ƴan ta'addan a dajin Kuduru ne na'urar leƙen asiri ya nuna akwai ƴan bindiga da dama a cikin gine-ginen da ke dajin.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An sace kofin gasar kwallon Afrika AFCON a hedkwatar CAF

A cewarsa, rundunar dakarun saman ta NAF ta aike da jiragen yaƙi da jirgi mai saukan ungulu masu ɗauke da bindiga zuwa wurin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel