Yanzu-yanzu: Najeriya ta karbi rigakafin COVID-19 daga ƙasar Rasha (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Najeriya ta karbi rigakafin COVID-19 daga ƙasar Rasha (Hotuna)

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a ranar Juma'a ta karbi samfurin rigakafin cutar korona na ƙasar Rasha.

Jakadan Rasha a Najeriya, Alexey Shebarshin ne ya mika wa ministan lafiyar Najeriya, Osagie Ehanire rigakafin yayin ziyarar da ya kai ma'aikatar lafiyar a Abuja.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ma'aikatar, Olujimi Oyetomi.

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta barki rigakafin COVID-19 daga ƙasar Rasha
Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta barki rigakafin COVID-19 daga ƙasar Rasha
Asali: Twitter

An yi wa sanarwar laƙabin da 'Jakadan Rasha a Najeriya, Alexey L. Shebarshin ya kawo rigakafin COVID-19 na Rasha yayin ziyarar da ya kai wa ministan lafiyar Najeriya.'

Yanzu-yanzu: Najeriya ta karbi rigakafin COVID-19 daga ƙasar Rasha (Hoto)
Yanzu-yanzu: Najeriya ta karbi rigakafin COVID-19 daga ƙasar Rasha (Hoto)
Asali: Twitter

A baya, The Punch ta ruwaito cewa shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasarsa ta amince da wani rigakafi da ke bayar da kariya daga coronavirus.

DUBA WANNAN: Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, daga baya ta ce za ta yi nazarin ingancin rigakafin.

Ehanire a ranar Juma'a ya ce ba tare da ɓata lokaci ba za a mika rigakafin ga Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, NAFDAC, da Cibiyar Binciken Magunguna ta Najeriya da wasu hukumomin don tabbatar da ingancinsa kafin a duba yiwuwar amfani da shi.

A cewar alƙallumar da hukumar daƙile cututtuka masu ƴaduwa ta Najeriya, NCDC ta fitar a daren Alhamis, fiye da mutum 50,000 ne suka kamu da coronavirus.

Alƙalluman sun kuma nuna kimanin mutum 1,000 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da cutar ta korona.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel