An kama jami'an LASTMA suna faɗa da fasinja saboda N100

An kama jami'an LASTMA suna faɗa da fasinja saboda N100

An dauki hotunan jami'an hukumar kula da dokokin tuki na jihar Legas, LASTMA, su biyu suna faɗa da fasinjoji a wani mota da suka fito daga Ikeja zuwa Obalende.

Jami'an na LASTMA da kayan aikinsu ke dauke da sunayen E.A. Fagbuyi da N. Oladega sun tare direban motan a toll gate na 7 up da ke kusa da Berger road a Legas.

Sun yi zargin cewa tun a makon da ya gabata ya ke canja hanya don kada ya hadu da su kuma suka bukaci ya biya su kuɗi saboda hakan.

An kama jami'an LASTMA suna faɗa da fasinja saboda N100
An kama jami'an LASTMA suna faɗa da fasinja saboda N100
Source: Twitter

Yaron motar (kwandasta) ya shaida wa wakilin Premium Times a cikin motar cewa suna neman direban ya basu toshiyar baki ta Naira 100 ne.

Sai dai lamarin ya ɗauki sabon salo bayan Fagbuyi ya karbe motar kuma ya nufa wata hanya daban ba inda fasinjojin za su tafi ba.

Daga nan ne kuma fasinjojin da ke cikin motar suka harzuƙa suka nuna ƙin amincewarsu da hakan ya janyo musayar kalamai har aka kaure da dambe.

An kama jami'an LASTMA suna faɗa da fasinja saboda N100
An kama jami'an LASTMA suna faɗa da fasinja saboda N100
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta amince da buɗe makarantu a Najeriya

A lokacin da ake damben ne jami'in hukumar ta LASTMA mai suna Mista Oladega ya yi wa wata fasinja mai suna Sandra duka ya kuma lalata mata fuskar wayar salular ta (sikirin).

Jami'an sunyi barazanar za su yi wa matar rauni saboda ta bukaci su biya ta kuɗin da za ta gyara wayar ta da shi kamar yadda Sandra ta shaida wa wakilin Premium Times da ke wurin da abin ya faru.

"An ci zarafi na kuma ba zan yarda ba. Ina amsa kira ne sai daya daga cikin jami'an ya zo ya kwace waya ta ya wurgar a ƙasa. Hakan yasa sikirin ɗin ya fashe. Wadannan mutanen ƴan daba ne kuma bai dace a ƙyalle su su cigaba da aiki a Legas ba," in ji Sandra.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel