Ganduje ya biya naira miliyan 257 don daukar nauyin dalibai 43 su tafi karatu kasar Misra

Ganduje ya biya naira miliyan 257 don daukar nauyin dalibai 43 su tafi karatu kasar Misra

- Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu akan a biya naira miliyan 257 ga daliban da aka ware za su tafi karatu kasar Misra

- Gwamnan ya ware mutane 43 da za a kai su kasar ta Misra domin yin karatu a bangarori daban-daban

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sanya hannu akan fitar da naira miliyan 257 wajen biyan kudin makaranta dana abinci ga dalibai 43 na jihar da za su tafi karatu kasar Misra (Egypt).

Sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis a Kano.

Anwar ya ce gwamnatin jihar Kano ce ta dauki nauyin daliban domin su yi karatu a fanni daban-daban a jami'ar Al-Mansoura da kuma jami'ar October 6 dake kasar ta Misra.

Ganduje ya biya naira miliyan 257 don daukar nauyin dalibai 43 su tafi karatu kasar Misra
Ganduje ya biya naira miliyan 257 don daukar nauyin dalibai 43 su tafi karatu kasar Misra
Source: Twitter

"Ganduje ya amince a fitar da naira miliyan 209 domin biyan kudin makarantar daliban da za suyi karatu a jami'ar Al-Mansoura.

"Haka kuma gwamnan ya sanya hannu akan biya naira miliyan 48 ga daliban da za suyi karatu a jami'ar October 6 dake kasar ta Misra," ya ce.

Anwar ya bayyana cewa gwamnan ya yafewa daliban duk da shiga harkar siyasa da suka yi.

KU KARANTA: An yiwa wasu yara guda 2 kyautar naira miliyan 43, bayan an iske su suna aikin makaranta a wajen sayar da abinci

"37 daga cikin daliban da za suyi karatu a Al Mansoura, sun rubuto takarda ga gwamna akan ya yafe musu, kan cewa suna dana sanin yadda aka yaudare su a harkar siyasa."

A cewar shi, gwamnan ya kuma dauki wasu aiki, inda za su dinga bin diddigin yadda ake biyan alawus-alawus na daliban cikin gida, domin magance wahalar da suke fuskanta kan cutar COVID-19.

Anwar ya kara da cewa an umarci hukumar kula da karatun daliban ta jiha da ta fara yiwa daliban rijista, inda ake sa ran za a biya musu kudin makaranta kafin a bude makarantu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel