Tashin hankali: Wani mutumi ya fillewa mahaifiyarshi kai da takobi ya boye kan a cikin firji

Tashin hankali: Wani mutumi ya fillewa mahaifiyarshi kai da takobi ya boye kan a cikin firji

Wani mutumi ya sare kan mahaifiyarshi da takobi ya boye kan a cikin firji, kamar yadda kotu ta bayyana

Mutumin mai suna Phillip Tarver, mai shekaru 47, ya kaiwa Angela Tarver hari, ya kuma yiwa mahaifinsa mai shekaru 83 barazana a gidansu dake Woking, Surrey, a ranar 19 ga watan Disamba, 2019.

Kotun ta samu labarin cewa Philip Tarver ya sha kwalbar Vodka guda daya da kuma kwalbar giya guda shida a cikin wannan daren da yayi wannan aika-aika.

A lokacin da mahaifinsa Colin ya tashi daga bacci, yaga danshi sanye da kayan mata. Bayan ya gama hada abincin safe, Colin ya jiyo matarsa na ihu.

Tashin hankali: Wani mutumi ya fillewa mahaifiyarshi kai da takobi ya boye kan a cikin firji
Tashin hankali: Wani mutumi ya fillewa mahaifiyarshi kai da takobi ya boye kan a cikin firji
Source: Facebook

Da take bayani akan lamarin a Old Bailey, Alexandra Healy QC ta ce: "A cikin wajen dafa abinci, ya cakawa mahaifiyarsa wuka a kirji, inda ya kasheta.

"Bayan haka ya yiwa mahaifinsa barazanar kisa."

Ms Hailey ta kara da cewa: "Ya jiyo ihu, sai ya garzaya daga inda yake zuwa wajen cin abincin.

"Ya ga kujerar da Angela ke zaune ta fadi. Ya gano kafar matarsa ta saki a kasa kuma bata motsi.

"Ya kuma ga cewa tana kwance rub da ciki. Kawai sai ganin dan nashi yayi a gabanshi rike da takobin shi da ya mallaka lokaci mai tsawo.

"Rike da takobin a gaban shi yace 'zan kashe ka' ko kuma 'sai na kashe ka'.

A hankali mahaifin ya samu ya karbe takobin daga hannun shi, kafin ya sanar da 'yan sanda.

KU KARANTA: Tashin hankali: 'Yan ruwa sun kashe budurwa a lokacin da ake yi mata wankan shiga addinin Kirista

Ms Healy ta ce: "An gano cewa, kafin 'yan sandan su karaso gidan, Phillip ya yanke kan mahaifiyarsa ya sanya a cikin firji.

"Haka kuma ya yanke dan yatsan da take sanye da zobe, ya sanya a cikin butar karfe."

Daga baya ya fara gyara wajen, ya wanke kanshi tare da wukar da yayi amfani da ita wajen wannan aika-aika.

Bayan 'yan sanda sun zo wajen sai ya fito wajen yace musu ya saduda, cewar Ms Healy.

Bayan an kama shi, Philip ya jiyo mahaifinsa yana magana da 'yan sanda akan cewa matarsa na cikin firji.

Bayan zuwa ofishin 'yan sandan, sai ya ce yana dana sanin kashe ta.

Bayan gabatar da gwaje-gwaje na kwakwalwa, an kai Tarver asibitin mahaukata inda aka tsare shi har zuwa watan Maris, har zuwa lokacin da aka tabbatar ya isa yin magana da 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel