Bamu yarda da karin farashin man fetur ba - Marasa rinjaye a majalisar wakilai

Bamu yarda da karin farashin man fetur ba - Marasa rinjaye a majalisar wakilai

Marasa rinjaye a majalisar wakilan tarayya sun bayyana rashin amincewarsu da karin farashin litan man fetur daga N148 zuwa N151.56 da kamfanin man feturin Najeriya NNPC tayi ranar Laraba.

Yan majalisan, a jawabin da shugabansu, Hanarabul Ndudi Elumelu yayi, ya cewa ba zasu taba amincewa da wannan kari ba saboda zai sabbaba hauhawar kayan masarufi da abubuwa kuma zai tsananta halin kuncin da yan Najeriya ke ciki.

A cewar Elumelu: "Marasa rinjaye a majalisar wakilan tarayya sun bayyana rashin amincewarsu da karin farashin man fetur ta aka sanar."

"Dalilin haka shine hakan zai tsananta halin kuncin da al'ummarmu ke ciki, musamman a yanzu da yawancin yan Najeriya ke kokarin rayuwa cikin wahala sakamakon tsadan abubuwa da matsalar tattalin arziki."

Yan jam'iyyar adawan sun kalubalanci jam'iyyar APC cewa maimakon karar kudin man fetur, kamata yayi su nemo hanyar da zai saukar da farashin irinsu farfado da matatin man Najeriya.

Bamu yarda da karin farashin man fetur ba - Marasa rinjaye a majalisar wakilai
Bamu yarda da karin farashin man fetur ba - Marasa rinjaye a majalisar wakilai
Source: Twitter

Legit ta kawo muku rahoton cewa Farashin man fetur ya karu zuwa N151.1 ga lita, a cewar kamfanin kasuwancin man fetur PPMC, wani sashen kamfanin man feturin Najeriya NNPC.

A takardar da jaridar Vanguard ta bayyana cewa ta samu gani, D.O Abalaka na kamfanin PPMC yace: "Ku sani cewa mun daura sabon farashin mai a shafin rubuta kudi."

"A yanzu, farashin man fetur PMS zai koma naira dari da hamshin da daya, da kwabo hamsin da shida ga lita."

"Za'a fara aiki da sabon farashin daga 2 ga Satumba, 2020."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel