Bayan Legas, Osun, Delta da Kogi, jihar Anambara ta sanar da ranar bude makarantun sakandare da firamare

Bayan Legas, Osun, Delta da Kogi, jihar Anambara ta sanar da ranar bude makarantun sakandare da firamare

Makarantun firamare da sakandare a jihar Anambara zasu bude ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, 2020, bisa jawabin da sakataren din-din-din na ma'aikatar ilimin jihar, Nwabueze Nwanko ya saki a Awka, babbar birnin jihar.

Bayanan da yayi sun nuna cewa za'a fara karatun zangon karshe ranar 14 ga Satumba kuma a kammala ranar Juma'a, 23 ga Oktoba, 2020 ga makarantun firamre da sakandare.

Ya ce wadanda ke makarantun kwana kuma zasu koma ranar 5 ga watan Satumba kafin saura.

Jawabin ya ce an kayyade ranar da za'a yi karatu ne saboda a kammala zangon da wuri.

"Mun cigaba da karantar da yaranmu ta hanyar yanar gizo, da kuma rediyo. Za mu cigaba da hakan yayinda muke kokarin bude makarantun kadan-kadan kuma muna lura da lamarin." Yace

"Muna kira ga iyaye su samawa yaransu sinadarin tsaftace hannu da takunkumin rufe baki."

Bayan Legas, Osun, Delta da Kogi, jihar Anambara ta sanar da ranar bude makarantun sakandare da firamare
Bayan Legas, Osun, Delta da Kogi, jihar Anambara ta sanar da ranar bude makarantun sakandare da firamare
Asali: Depositphotos

Ga jerin jihohi 4 da suka sanar zasu bude makarantunsa da ranakun kawo yanzu:

1. Jihar Kogi

Gwamnatin jihar Kogi a ranar Talata ta sanar da cewa dukkan makarantu mallakin gwamnatin jihar zasu koma aiki ranar 14 ga watan Satumba, 2020.

Kwamishanan ilimin jihar, Mista Wemi jones, ya ce makarantun sun hada da Firamare, Sakandare da na gaba da sakandare.

Ya sanar da hakan ne ranar Talata, 1 ga Satumba, a Lokoja yayin hira da manema labarai

A cewar jones, gwamnatin jihar ta yanke shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

2. Jihar Delta

Jami'o'i a jihar Delta zasu koma bakin aiki ranar 21 ga Satumba, 2020, watanni biyar bayan rufesu domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Majiyoyi daga gwamnatin jihar sun bayyana cewa an yarje da komawan dalibai makarantar ne bayan ganawar gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa da masu ruwa da tsaki.

3. Jihar Legas

A ranar 29 ga Agusta, 2020, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bada umurnin bude dukkan jami'o'i mallakan gwamnatin jihar daga ranar 14 ga Satumba, 2020.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai yau Asabar, kamar yadda TheCable ta shaida.

Hakazalika ya bayyana cewa da yiwuwan za'a bude makarantun sakandaren jihar fari daga ranar 21 ga Satumba, 2020.

An rufe makarantun ne a watan Maris sakamakon bullar cutar Korona.

Jihar Legas ke kan gaba wajen yawan adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya.

4. Jihar Osun

Gwamnatin jihar Osun ta sanar da ranar bude makarantun jihar.

Kwamishanar ilimin jihar, Funke Egbemode, ta sanar da hakan ne ranar Litinin inda tace za'a bude ranar 21 ga Satumba, 2020.

A cewarsa, an yanke shawarar haka ne a zaman majalisar zartaswar jihar.

Ta yi kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa an shirya makaman bude makarantun bisa ka'idojin da ma'aikatar Ilimi ta gindaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel