Yanzu-yanzu: Ƴan fashi sun kai hari gidan Abiola a Legas

Yanzu-yanzu: Ƴan fashi sun kai hari gidan Abiola a Legas

Wasu mutane dauke da bindigu da har yanzu ba a san ko su wanene ba sun afka gidan Moshood Abiola da ke Ikeja a Legas.

Yan fashin sun sace kudade masu yawa na ƙasashe daban-daban da a halin yanzu ba a tabbatar da adadin su ba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Ƴan bindiga sun kai hari gidan Abiola a Legas
Yanzu-yanzu: Ƴan bindiga sun kai hari gidan Abiola a Legas
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

A wata takardar da aka fitar a madadin iyalan, Tundun Abiola, diyar marigayin dan attajirin kasuwar ta ce, sun yi rahoto wurin 'yan sanda kuma an fara bincike a kan lamarin.

Ta ce 'yan bindigar sun matukar azabtar da iyalan tare da hantararsu. Tundun ta kara da cewa, barayin sun kwashe kudi da wasu kadarori daga gidan bayan kutsawarsu.

"'Yan bindigar sun gallazawa iyallan tare da hantararsu inda suka kwashe kudi da wasu kadarori a gidan," takardar tace.

"Tuni muka sanar da 'yan sanda. Ana bincikar aukuwar lamarin. Hankalinmu ya kwanta ganin cewa babu rai da aka rasa yayin mummunan lamarin.

"Muna godiya ga Allah kuma muna mika godiyarmu ga 'yan uwa da abokan arziki a fadin duniya da suka kira tare da turo mana sakonnin jaje," in ji ta.

Abiola ya ci zaben shugabancin kasa da aka yi a Najeriya a shekarar 1993, wanda gwamnatin mulkin soji karkashin shugabancin Ibrahim Babangida ta soke.

A 2018, shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya amince da mayar da ranar damokaradiyya ta kasar nan zuwa ranar 12 ga watan Yuni don karrama Abiola, wanda ya karrama shi a kasar nan duk da bashi da rai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel