Zaɓen Edo: APC ta dakatar da yaƙin neman zaɓe bayan wasu magoya bayanta sun mutu a hatsarin mota

Zaɓen Edo: APC ta dakatar da yaƙin neman zaɓe bayan wasu magoya bayanta sun mutu a hatsarin mota

- Wasu magoya bayan jam'iyyar APC a jihar Edo sun mutu sakamakon mummunan hadarin mota

- An ruwaito cewa hatsarin ya ritsa ne da tawagar tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole

- An kuma ce ƴan sanda biyu sun mutu sakamakon hatsarin motar da ya afku a Benin City

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a ranar Talata 1 ga watan Satumba ta soke taron yaƙin neman zaɓe da ta shirya yi bayan hadarin mota da ya ritsa da magoya bayan ta da wasu ƴan sanda.

An shirya ƴin taron yaƙin neman zaben ne da nufin janyo hankalin masu zabe a garin ta Usen su zabi jam'iyyar ta APC.

Mai magana da yawun kwamitin kamfen din APC, John Maiyaƙi, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce trela ce da bi ta kan wasu motocci a tawagar jiga-jigan jam'iyyar ciki har da tsohon shugaban jam'iyyar na ƙasa, Adams Oshiomhole kafin Ojukwu junction a Benin City, babban birnin jihar.

Zaɓen Edo: APC ta dakatar da yaƙin neman zaɓe bayan wasu magoya bayanta sun mutu a hatsarin mota
Zaɓen Edo: APC ta dakatar da yaƙin neman zaɓe bayan wasu magoya bayanta sun mutu a hatsarin mota
Asali: Facebook

Ya kuma ce jam'iyyar to soke taron domin mutunta wadanda suka rasu sakamakon hatsarin motar kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Maiyaƙi ya yi wa iyalan wadanda suka rasu ta'aziyya a madadin Pastor Ize-Iyamu da jam'iyyar ta APC inda ya ce, "muna taya su baƙin ciki"

Ya yi alƙawarin cewa kwamitin yaƙin neman zaben za ta yi iya ƙoƙarinta ta rage musu raɗaɗin rashin wadanda suka rasa.

Ya kuma tabbatar wa iyalan ƴan sandan da suka rasu haɗarin motar cewa gwamnatin Edo ba za ta taɓa manta wa da sadaukarwa da su kayi ba.

DUBA WANNAN: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

Maiyaƙi ya bukaci magoya bayan jam'iyyar su yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma kiyayye afkuwar irin wannan ƙadarar a gaba.

Kazalika, jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta bukaci rundunar ƴan sanda ta yi kama Mista Kabiru Adjoto da Osaigbovo Iyoha ta gudanar da bincike a kansu.

Mutanen biyu dukkansu hadiman gwamnan jihar Godin Obaseki ne.

Shugaban APC na jihar, Kwanel David Imuse, a ranar Talata 25 ga watan Agusta yayin taron manema labarai ya bukaci a kama su saboda ɗaukan nauyin ƴan daba da suka kai hari harabar Majalisar Jihar a makon da ta gabata.

Imuse ya bukaci ƴan sanda su kama su nan take su fara bincike a kansu domin ba su da kariya daga kundin tsarin mulki da zai hana a gurfanar da su a halin yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel