Ba zamu taba amincewa da kara farashin wutan lantarki ba - Kungiyar Kwadago, NLC

Ba zamu taba amincewa da kara farashin wutan lantarki ba - Kungiyar Kwadago, NLC

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta ce sabon karin farashin wutan lantarkin da da kamfanin raba wutan Abuja AEDC ya sanar ba zai yiwu ba, kuma dukkan ma'aikatan Najeriya za suyi fito na fito da hakan.

NLC a jawabin da shugabanta, Ayuba Wabba, ya rattafa hannu ya siffanta karin farashin matsayin "cin zalin talakawan Najeriya", kuma ya ya gargadi kamfanonin wuta kada suyi tunanin farawa.

Yace: "Kamfanin raba wutan lantarkin Abuja AEDC ta daura rawanin kunya yayinda ta sanar da sabon shirin kara farashin wutan lantarki ga jama'an dake yankunansu."

"Sun sanar da hakan duk da cewa umurnin majalisar dattawan Najeriya na cewa kada su kara da umurnin shugaban kasa cewa kamfanonin lantarki su dakatad da shirin kara farashin."

"Bamu da masaniya kan wani umurni daga gwamnati ko wani zababben shugaban da ya soke umurnin da aka bada na kara tsanantawa aljihun yan Najeriya ta hanyar kara farashin wutan lantarki."

Wabba ya kalubalanci hukumar lura da wutan lantarki a Najeriya (NERC), ta fito tayi magana kan wannan don kare hakkin yan Najeriya.

Ba zamu taba amincewa da kara farashin wutan lantarki ba - Kungiyar Kwadago, NLC
Ba zamu taba amincewa da kara farashin wutan lantarki ba - Kungiyar Kwadago, NLC
Asali: Depositphotos

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa NERC ta sanar cewa za'a fara dabbaka karin farashin wutan lantarki fari daga ranar 1 ga Satumba, 2020 (Yau kenan).

Hakan ya zo watanni uku bayan majalisar dokokin tarayya ta hana kara farashin wutan lantarkin ranar 1 ga Yuli, 2020 saboda halin talaucin da yawancin yan Najeriya ke ciki.

Amma a takardar da kamfanonin wutan lantarki suka rika saki yau Talata, an ga karin farashin da akayi ga masu samun wuta sama da sa'o'i 12 a rana.

A cewar takardar, sabon farashin na dangane da adadin sa'o'in da mutum ke samu a ranar.

An tsara sabon yanayin farashin wutan ne bisa masu yawan samun wuta da marasa samu sabanin tsohon tsarin gidaje, kasuwanni da masana'antu.

A takardar da The PUNCH ta samu, kamfanin raba lantarkin Ikeja Electric, ta yi tsarinta kan kwastamomi masu samun wuta sama da sa'o'i 12 a ranar zasu rika biyan N42.73/KWh, sabanin N21.30 / kWh da aka biya yanzu.

Kamfanin lantarkin Eko kuwa, kwastamomi masu samun wuta sama da sa'o'i 12 a ranar zasu rika biyan N43.01/KWh, sabanin N24 kWh da ake biya yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel