Da duminsa: Karin farashin wutan lantarkin da akayi zai fara aiki yau - NERC

Da duminsa: Karin farashin wutan lantarkin da akayi zai fara aiki yau - NERC

Hukumar lura da wutan lantarki a Najeriya (NERC), ta sanar cewa za'a fara dabbaka karin farashin wutan lantarki fari daga ranar 1 ga Satumba, 2020 (Yau kenan).

Hakan ya zo watanni uku bayan majalisar dokokin tarayya ta hana kara farashin wutan lantarkin ranar 1 ga Yuli, 2020 saboda halin talaucin da yawancin yan Najeriya ke ciki.

Amma a takardar da kamfanonin wutan lantarki suka rika saki yau Talata, an ga karin farashin da akayi ga masu samun wuta sama da sa'o'i 12 a rana.

A cewar takardar, sabon farashin na dangane da adadin sa'o'in da mutum ke samu a ranar.

An tsara sabon yanayin farashin wutan ne bisa masu yawan samun wuta da marasa samu sabanin tsohon tsarin gidaje, kasuwanni da masana'antu.

A takardar da The PUNCH ta samu, kamfanin raba lantarkin Ikeja Electric, ta yi tsarinta kan kwastamomi masu samun wuta sama da sa'o'i 12 a ranar zasu rika biyan N42.73/KWh, sabanin N21.30 / kWh da aka biya yanzu.

Kamfanin lantarkin Eko kuwa, kwastamomi masu samun wuta sama da sa'o'i 12 a ranar zasu rika biyan N43.01/KWh, sabanin N24 kWh da ake biya yanzu.

KU KARANTA: Kada ka sake baiwa Buhari daman karban bashi - Atiku ga Ahmad Lawan

Da duminsa: Karin farashin wutan lantarkin da akayi zai fara aiki yau - NERC
Da duminsa: Karin farashin wutan lantarkin da akayi zai fara aiki yau - NERC
Asali: Twitter

A makon da ya gabata, mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin baiwa dukkan yan Najeriya mitan wutan lantarki domin kawar da tsarin da ake kai yanzu na raba 'Bill' na kiyasi.

A takardar da aka saki ranar Laraba, shugaban hukumar lura da wutan lantarki a Najeriya (NERC), James Momoh, ya ce hakazalika shugaba Buhari ya bada umurnin kara farashin wutan.

Amma Momoh yace za'a togaciye "Talakawan" Najeriya daga karin farashin da za'ayi.

Shugaban NERC ya ce karin kudin ba zai shafi wadanda ake rabawa 'Bill' na kiyasi ba har yanzu har sai sun samu mita.

Zaku tuna cewa a watan Junairu, hukumar NERC ta sanarwa yan Najeriya cewa za'a kara farashin wutan lantarki daga watan Afrilu.

Amma aka dakatar da yin hakan saboda bullar annobar Korona a watan Maris.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel