Katsina da Zamfara: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 2, sun damke 12

Katsina da Zamfara: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 2, sun damke 12

Dakarun rundunar Operation Sahel Sanity sun kashe 'yan bindiga biyu, sun damke 12 daga ciki tare da ceto wasu jama'a masu yawa da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Zamfara a makon da ya gabata.

Wannan na kunshe ne a wata takardar da mukaddashin daraktan yada labarai na hukumar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya fitar a ranar Litinin.

Onyeuko ya ce, "A ranar 28 ga watan Augustan 2020, dakarun sojin Najeriya da ke Maru sun kai wa wasu da ake zargin 'yan bindiga samame yayin da suke kokarin shiga kauye Gobirawa.

"Cike da kwarewar dakarun tare da taimakon 'yan sa kai, sun hana 'yan bindigar shiga kauyen.

"A yayin samamen, dakarun sun yi musayar wuta da 'yan bindigar inda suka kashe biyu daga ciki, amma wasu sun tsere da miyagun raunika. An ga jini a kasa wanda ya bayyana hanyar da suka bi.

"A wannan ranar, dakarun sun kai samame wata maboyar 'yan bindigar da ke kauyen Gamji. A yayin samamen, an kama 'yan bindiga shida sannan an samo bindiga daya, babur daya da adduna biyu.

“Dakarun sojin da aka kai Zakka, sun damke wasu 'yan bindiga uku bayan bayanan sirri da suka samu. Sun damke Sagir Garba, Hafizu Mato da Suleiman Sada.

Katsina da Zamfara: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 2, sun damke 12
Katsina da Zamfara: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 2, sun damke 12. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin jiga-jigan APC da ke zawarcin shugabancin jam'iyyar da manyan mukamai

"Wandanda ake zargin sun shiga hannu ne bayan wasu mafaruta sun tona asirin kungiyarsu a matsayin wacce ta addabi yankin.

"Binciken farko da aka yi, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu na hannu a cikin satar shanu da ake yi a yankunan kauyukan Kwaya, Sabon Birni da Baure."

Sauran wadanda ake zargin kuma dakarun suka damke, sun hada da Lawali Dahiru, Bello Abdurrahman da Zaiyanu Kaura, wadanda aka bayyana a matsayin shugabbnin 'yan bindigar da suka addabi yankin arewa maso yamma na kasar nan.

Janar Onyeuko ya kara da bayyana cewa, dukkan wadanda suka ceto a halin yanzu sun sadu da 'yan uwansu.

"A halin yanzu ana bincikar dukkan wadanda aka kama kuma ana amfani da bayanansu wurin damko 'yan uwansu," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel