Hotunan Tinkiya mafi tsada da aka taba siyarwa a duniya, an siyeta a N190m
Wata Tinkiya da wasu iyalai suka kiwata a garin Stockport da ke Ingila ta janyo cece-kuce. An yi gwanjonta inda aka siyar da shi a kan kudi har $490,000 wanda daidai yake da N190,000 miliyan.
Iri tinkiyar mai suna Texel a halin yanzu shine mafi tsada a fadin duniya., shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Tinkiyar mai suna Diamond an siyar da ita a makon nan bayan Charlie Boden da iyalansa sun yi kiwonta a gonarsu ta Mellor Hall.

Asali: Twitter
A yayin gwanjon tinkiyar da aka yi, an fara da taya ta a kan $9,000 amma babu jimawa aka kaita har $490,000.

Asali: Twitter
Wasu manoman 'yan kasuwa ne suka siya dabbar inda suke so su raineta tare a gonarsu domin samun irinta.
Kungiyar kula da tumakin irin Texel, ta ce wannan ta karya tarihin da wata tinkiyar ta kafa a 2009 wacce aka siyeta a kan kudi har pam 231,000.
KU KARANTA: Hira da mahaifin jaruma Fadila Muhammad: Ya bayyana ciwon da ya kasheta

Asali: Twitter
Kamar yadda kungiyar ta sanar, an fara samun irin tinkiyar Texel ne a wani tsibiri mai suna Texel.
Daya ne daga cikin tsibirran Holland amma yanzu tumakin Ingila sun mamaye yankin.
Jeffe Aiken, daya daga cikin manajojin gonar Procters, kuma daya daga cikin masu bukatar siyan tinkiyar, ya ce: "A tun farko dai Texel shine irin tumaki mafi kyau a Ingila. In kana son tumaki masu matukar nagarta, ka gwada siyansu.
"Dabba ce daban ba irin kowacce ba. A cikinsu wannan ce mafi nagarta da na taba gani. Muna fatan zai kasance hakan."

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng