Kungiyar kwallon Arsenal ta lallasa Liverpool don lashe farentin Community Shield

Kungiyar kwallon Arsenal ta lallasa Liverpool don lashe farentin Community Shield

Kungiyar kwallon Arsenal ta lallasa Liverpool kwallo 5 zuwa 4 a fenariti bayan yin kunnen jaki tsawon mintuna 90 a wasan da aka buga a filin kwallo Wembely.

Kungiyar ta lashe farentin al'ummar Birtaniya wanda aka fi sani da Community Shield.

Tsohon zakaran yan kwallon nahiyar Afrika, Pierre-Emerick Aubameyang, ya fara zura kwallo ragar Liverpool a minti na 12.

Sai da aka kusa tashi wasa Takumi Minamino na kungiyar Liverpool ya mayar da martani da kwallo a minti na 73.

A haka aka cigaba da karawa babu wanda ya kara zura kwallo cikin kungiyoyin biyu har minti 90 ya kare.

Yayinda aka shiga fenariti, yan kwallon Arsenal sun daki raga a dukkan biyar da suka buga, hakazalika Liverpool illa Riham Brewster wanda ya tashi tsintsaye maimakon dukan zare.

Ana buga wasan Community Shield ne tsakanin wadanda suka lashe kofin Firimiya da wadanda suka lashe FA.

Arsenal ta doke Chelsea ne a wasan karshe Firimiya yayinda Liverpool tayiwa kora zarra ta lashe kofin Firimiya.

Kalli hotuna:

Kungiyar kwallon Arsenal ta lallasa Liverpool don lashe farentin Community Shield
Kungiyar kwallon Arsenal ta lallasa Liverpool don lashe farentin Community Shield
Asali: Getty Images

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel