Kada ka sake baiwa Buhari daman karban bashi - Atiku ga Ahmad Lawan

Kada ka sake baiwa Buhari daman karban bashi - Atiku ga Ahmad Lawan

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya aike wasika ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, inda ya bukaci majalisar kada ta sake baiwa Buhari daman karban basussukan da ba zasu haifar da 'da mai ido ba.

A wasika mai ranar watan 25 ga Agusta, Atiku ya yi kira da yan majalisar dokokin tarayya su tsagaita baiwa Buhari daman karban bashin da ba zai kawo kudi ba.

Ya ce Najeriya za ta iya shiga mawuyacin hali idan aka cigaba da karban basussuka saboda wadanda aka karba ba abubuwan kwarai akayi da su ba.

A cewar ofishin kula da basussukan Najeriya DMO, bashin da ake bin Najeriya kawo Maris 2020 ya kai $79.3 billion.

Za ku tuna cewa a watan Yuni, Ahmad Lawan ya sanar da cewa mambobin majalisan dokokin tarayya sun amince Buhari ya karbi bashin $28 billion.

KU KARANTA: Ku bamu milyan 20 mu saki yaranku: Masu Garkuwa da dalibai a Kaduna sun bukaci kudin fansa

Kada ka sake baiwa Buhari daman karban bashi - Atiku ga Ahmad Lawan
Kada ka sake baiwa Buhari daman karban bashi - Atiku ga Ahmad Lawan
Asali: Facebook

A wasikar Atiku yace: "A ranar 29 ga Mayu, 2015, bashin da Najeriya taci ya kai Tiriliyan 12. Amma yanzu Agusta 2020, bashin ya ninku sau uku zuwa N28.63 trillion."

"Abin damuwa a nan shine wadannan basussuka basu da muhimmanci kuma ba'a bukatarsu. Binciken da akayi kan abubuwan da akayi da kudaden ya nuna cewa ba wasu ayyukan kirki masu kawo kudi akayi da su ba."

"Saboda haka, a matsayinku na masu duba abubuwan da sauran bangarorin gwamnati ke yi, ina mai bukatan daga yanzu, kada majalisar dokokin tarayya ta kara bada daman karban sabon bashin da za'a yi amfani wajen ayyuka maras kawo kudi ko marasa amfani."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel