Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da hadarin jirgin sama da ya faru a Legas

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da hadarin jirgin sama da ya faru a Legas

A ranar Juma'a 29 ga watan Agustan 2020 ne wani jirgin sama mai saukan ungulu ya yi haɗari a Salvation Road, Opebi, Ikeja a jihar Legas.

Lamarin mai tayar da hankali ya yi sanadin rasa rayuka uku na wadanda ke cikin jirgin bayan jirgin ya faɗa kan wata katanga da ta raba wasu gidaje biyu a 16A, Salvation Road.

Ga dai wasu muhimman abubuwa 5 da ya dace ku sani game da hadarin kamar yadda The Nation ta tattaro:

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da hadarin jirgin sama da ya faru a Legas
Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da hadarin jirgin sama da ya faru a Legas
Asali: Original

1. Jirgin mai saukan ungulu, Bell 206-3 mai lambar rajista 5N-BQW mallakar Quorum Aviation ne.

2. Jirgin mallakar kamfanin sufurin ya taso ne daga Fatakwal, babban birnin jihar Rivers ɗauke da matuƙa biyu da fasinja guda ɗaya.

3. Saura kimanin mintuna biyu jirgin ya isa wurin da za shi wato filin tashin jirage na Murtala Muhammed da ke Ikeja, Legas.

DUBA WANNAN: Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya sabunta naɗin Ugbo da wasu mutum biyu a NDPHC

4. Matuƙan jirgin biyu sun mutu nan take, shi kuma mutum na uku a jirgin ya mutu daga baya a asibitin koyarwa da jami'ar Legas da ke Ikeja.

5. Cikin ikon Allah, jirgin bai yi sanadin mutuwar kowa ba a gidajen da ya faɗa bayan ya yi haɗarin.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin tarayya ta dage ranar dawo da zirga-zirgan jiragen waje wanda aka shirya yi a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta zuwa ranar 5 ga watan Satumba.

Legit.ng ta rahoto cewa ma’aikatar sufurin jirage ce ta sanar da hakan a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, a lokacin taron kwamitin fadar Shugaban kasa kan COVID-19, a Abuja, babbar birnin tarayyar kasar.

Ma’aikatar ta sanar da ci gaban ne a shafinta na twitter, @fmaviationg, inda ta ba ‘yan Najeriya hakuri a kan dagewar da ta yi.

“Da dumi-dumi: Muna danasanin sanar da cewar an dage dawo da zirga-zirgan jiragen sama da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Agusta zuwa ranar 5 ga watan Satumba 2020,” in ji ma’aikatar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel