Karin 'yan Najeriya 160 sun kamu da korona, jimilla 53,477
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 160 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:27 na daren ranar Jumaa 28 ga Agustan shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 160 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Asali: UGC
Plateau-44
Lagos-27
Katsina-18
Edo-15
FCT-14
Ondo-10
Oyo-9
Kwara-6
Abia-4
Nasarawa-4
Kano-3
Ekiti-2
Kaduna-2
Kebbi-1
Ogun-1
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Jirgi mai saukar ungulu ya afka wa wani gini a Legas
Jimillar wadanda suka kamu - 53,477
Jimillar wadanda suka warke - 41,017
Jimillar wadanda cutar ta kashe - 1,011
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng