Ku cika alƙawarin da ku ka ɗauka, Dicko ya gargadi sojojin da suka yi juyin mulki a Mali

Ku cika alƙawarin da ku ka ɗauka, Dicko ya gargadi sojojin da suka yi juyin mulki a Mali

Malamin addinin musulunci mai faɗa a ji a Mali kuma daya daga cikin jagoran zanga-zangar a kasar, Imam Mahmoud Dicko ya gargadi sojojin da suka kwace mulki su cika alƙawarin da suka ɗauka.

"Na yi kira ga dukkan mutane su haɗa kai domin ceto Mali, kuma har yanzu ina kira ga hakan amma wanann baya nufin sojojin 'suyi duk abinda suka ga dama," Dicko ya faɗa wa magoya bayansa.

"Ba za mu mika ragamar mulkin ƙasar nan ga wani ba ya yi duk abinda ya ga dama, wannan lokacin ya wuce," in ji shi.

Ku cika alƙawarin da ku ka ɗauka, Dicko ya gargadi sojojin da suka yi juyin mulki a Mali
Ku cika alƙawarin da ku ka ɗauka, Dicko ya gargadi sojojin da suka yi juyin mulki a Mali. hoto daga The Punch
Asali: Twitter

Bisa ga dukkan alamu sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Keita a ranar 18 ga watan Agusta sun bawa shugabansu ikon da shugaban ƙasa ke da shi.

Sai dai shugabannin kasashen Afirka ta Yamma sun nema a gudanar da zaɓe kana a mika mulki ga farar hula cikin watanni 12.

DUBA WANNAN: Buhari ya ware N13bn domin sabon tsarin 'yan sandan al'umma

Dicko ya ce akwai bukatar yin sauyin gwamnati a kasar ta Mali.

"Mu muka jagoranci gwagwarmayar," kamar yadda ya fadi a ranar Juma'a.

"Mutane sun mutu kuma ya zama dole sojojin da suka ƙarasa wannan aikin su rike alƙawarin da suka ɗauka."

A wani labarin daban Legit.ng ta ruwaito cewa Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya goyi bayan ECOWAS na bawa sojojin kasar Mali wa'adin wata 12 domin su mika mulki zuwa ga farar hula.

A ranar Juma'a, ne shugaba Buhari ya halarci taro na biyu ta yanar gizo na shuwagabannin kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS dangane da rikicin da ke faruwa a Mali.

Dukkannin shuwagabannin kasashen ECOWAS sun halarci taron, bisa jagorancin shugaban kungiyar ta ECOWAS, Jean-Claude Kassi Brou.

Shugabannin sun tattauna batutuwan a kan hanyoyin da za a kawo karshen rikicin siyasa da ya mamaye kasar ta Mali.

A karshen watannan ne dai wasu sojojin hamayya suka hambarar da gwamnatin shugaban kasa Ibrahim Keita, lamarin da ya ja ECOWAS ta cire kasar daga cikin kungiyar.

Sojojin da suka yi juyin mulkin sun bukaci yin shugabanci na tsawon shekaru uku kafin su mika mulki a hannun farar hula.

Sai dai, ECOWAS ta bayyana cewa ya zama dole sojojin su mika mulki zuwa hannun farar hula a cikin watanni 12, watau shekara daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164