An naɗa ɗan Najeriya Ministan Shari'a a Canada (Hotuna)
An naɗa wani ɗan Najeriya mazaunin ƙasar Canada, Kelechi Madu a matsayin ministan shari'a kuma babban alƙalin yankin Alberta da ke Canada.
Madu ya wallafa rubutu a shafinsa na Twitter a kan sabon mukamin da aka naɗa shi inda ya ce dama alƙalinci tana tabbatar da yi wa kowa adalci ne kuma hakan ba zai canja ba.
Madu ya ce yana girmama dokar ƴanci ta Canada naɗa ta ce:
"Babu bambanci tsakanin mutane a dokar ƙasa, doka ta bawa kowa ƴanci iri ɗaya ba tare da tsangwama ba ko banbanci."
Ya ce zai yi amfani da wannan kalaman domin kawo cigaba ga rayuwar mutanen yankinsa na Alberta.
Ya ƙara da cewa: "Ina fatan yin aiki domin kawo sauye-sauye ta demokradiyya da dokoki tare da tabbatar da aiwatar da su cikin adalci."
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Messi ya ce zai bar Barcelona

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
A wani labarin daban Shugaba Buhari ya rantsar da sakatarorin dindindin guda 12 kafin a fara taron Majalisar Zartarwa ta Kasa karo na 13 da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar intanet a Abuja.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya samu hallartar rantsarwar da aka yi a dakin taron majalisar da ke gidan gwamnati.
Sakatarorin da aka nada tun a watan Yuni cikin wata sanarwa da shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi Esan ta fitar suna hada da : Belgore Shuaib Mohammad Lomido, Kwara; Akinlade Oluwatoyin, Kogi; Ekpa Anthonia Akpabio, Cross River; Alkali Bashir Nura, Kano; Ardo Babayo Kumo, Gombe da Anyanwutaku Adaora lfeoma, Anambra.
Saura su ne Udoh Moniloja Omokunmi, Oyo; Hussaini Babangida, Jigawa; Mohammed Aliyu Ganda, Sokoto; Mahmuda Mamman, Yobe; Meribole Emmanuel Chukwuemeka, Abia daTarfa Yerima Peter, Adamawa.
Shugaban kasar ya kuma rantsar da kwamishinonin hukumar kula da maaikatan gwamnatin tarayya, Idahagbon Henry, da na hukumar tattara haraji da rabar da ita, Usman Hassan.
Ministocin da suka hallarci taron a zahiri sune: Godswill Akpabio, Niger Delta; Abubakar Malami, Ministan sharia; Alhaji Lai Mohammed, ministan labarai; Hajiya Zainab Ahmed, ministan kudi da tsare tsaran kasa; Mohammed Bello, minsitan Abuja, Sulieman Adamu, ministan albarkatun ruwa.
Saura da suka hallarci taron sune (SGF), Boss Mustapha; shugaban maaikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da mashawarcin shugaban kasa kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (murabus).
Shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Yemi Esan da sauran ministocin sun hallarci taron ne ta hanyar intanet daga ofisoshinsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng