Daga karshe, hukumar lafiya duniya WHO ta ce cutar shan inna ta kare a Najeriya

Daga karshe, hukumar lafiya duniya WHO ta ce cutar shan inna ta kare a Najeriya

Daga karshe, hukumar tabbatar da karewar cutar shan inna a nahiyar Afrika ARCC ta alanta cewa Najeriya da sauran kasashen Afrika sun barranta daga cutar shan inna a ranar Talata.

A cewar hukumar lafiyan duniya WHO, wannan ya kawo karshen muguwar cuta na biyu a nahiyar Afrika bayan cutar karambau shekaru 40 da suka gabata.

A karni na 20, cutar karambau ta bulla a Najeriya amma bayan samun rigakafi ya fara raguwa.

Amma yayinda wasu kungiyoyi suka fara yaki da yiwa yara rigakafi, cutar ta kara dawowa kuma WHO ya fara sabon yaki kafin aka samu nasara a shekarar 1980.

Shugabar ARCC, Rose Leke, ta bayyana cewa: "Yau rana ne mai tarihi a nahiyar Afrika. Hukumar tabbatar da karewar cutar shan inna a nahiyar Afrika ARCC na farin cikin sanar da cewa nahiyar ta samu nasarar cika sharrudan kawar da cutar shan inna, tun da an kwashe shekaru hudu babu mai cutar shan inna,"

ARCC ta sanar da hakan ne bayan shekaru da yawa suna bibiyan lamarin shan inna, suna bayar da rigakafi.

A 1996, shugabannin kasashen Afirka sun lashi takobin kawo karshen shan inna a taron kungiyar hada kan kasashen Afirka OAU da ya gudana a Yaounde, kasar Kamaru.

A lokacin, cutar shan inna na nakasa yara 75,000 kowani shekara a nahiyar.

Shekarar 2016 ne karshe da aka samu mai cutar shan inna a Najeriya.

Daga karshe, hukumar lafiya duniya WHO ta ce cutar shan inna ta kare a Najeriya
Daga karshe, hukumar lafiya duniya WHO ta ce cutar shan inna ta kare a Najeriya
Asali: UGC

KU KARANTA: Da na shiga matsala, Nasir El-Rufai ne ya fara taimakona inji Muhammadu Sanusi II

A bangare guda, Bayan watanni takwas da bullarta a duniya, an samu rigakafin cutar Coronavirus na farko a duniya, Shugaban kasar jamhurriyar Rasha, Vladimir Putin, ya alanta.

Valdimir Putin ya ce ya amince da fara yiwa mutane alluran rigakafin saboda yana aiki sosai, kuma tuni an yiwa diyarsa.

A cewar Reuters, Rasha ce kasa ta farko a duniya da ta bada umurnin fara amfani da rigakafi a duniya, watanni biyu kacal bayan fara gwaji.

Yayinda yake magana a wata ganawa, Putin ya ce cibiyar Gamaleya ta kasar ce ta samar da rigakafin kuma yana bada kariya daga cutar Korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel