Mailafiya ya ki amsa gayyatar Yan sanda, ya garzaya kotu

Mailafiya ya ki amsa gayyatar Yan sanda, ya garzaya kotu

Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Dakta Obadiah Mailafia ya garzaya Babban Kotun da ke Jihar Plateau domin neman a kare masa hakkinsa na walwala da adalci bayan da yan sanda suka gayyaci shi zuwa Abuja.

An hasashen cewa gayyatar da yan sanda suka yi wa Mailafia ba za ta rasa nasaba da gayyatar da Hukumar Yan Sandan Farar Kaya, DSS, ta masa ba a kan ikirarin da ya yi na cewa wani gwamnan arewa na cikin shugabannin Boko Haram.

Da ya ke jawabi yayin taron manema labarai a ranar Litinin 24 ga watan Agusta, Mailafia ya ce gayyatar da aka yi masa bita da kulli ne, cin mutunci, cin zarafi da yunkurin a bashi tsoro.

Mailafiya ya ki amsa gayyatar Yan sanda, ya garzaya kotu
Mailafiya ya ki amsa gayyatar Yan sanda, ya garzaya kotu. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas

Ya bayyana cewa zai shigar da kara a kotu domin kallubalantar gayyatar da rundunar yan sandan ta yi masa kamar yadda Linda Ikeji Blog ta ruwaito.

A wani rahoton baya bayan nan, Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa Rundunar Yan Sandan Najeriya ta aike wa Dakta Mailafia takardar gayyata zuwa Abuja.

Ƴan sandan za su fara binciken su ne duk da cewa hukumar ƴan sandan farin kaya, DSS, tana gudanar da nata binciken a kan zargin da tsohon mataimakin gwamnan CBN ɗin.

Sai dai rundunar ta ƴan sanda ba ta ambaci dalilin gayyatar sa ba a cikin takardar da ta aike masa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mataimakin kwamishinan ƴan sanda, Umar Sanda ne ya saka hannu a kan wasikar a madadin mataimakin Sufeta Janar na ƴan sanda, sashin masu binciken manyan laifuka, CID, da ke Abuja.

A takardar mai lamba 3000/X/FHQ/ABJ/VOI/245/8, mai ɗauke da kwanan wata 20 ga watan Agusta, ƴan sandan sun bukaci Mailafia ya zo ofishin hukumar sashin masu binciken manyan laifuka, Garki Area 10 Abuja a ranar Litinin 24 ga watan Agustan 2020 da karfe 11 na safe.

Takardar mai laƙabin "Ayyukan bincike, Binciken ƴan sanda tana ɗauke sa gargadin cewa abin sirri ta ke ɗauke da shi kuma duk wanda ya fallasa abinda ta ke ɗauke da shi zai iya fuskantar hukunci."

Saƙon da ke jikin wasikar ya ce, "muna sanar da kai cewa wannan ofishin na bincike a kan wani lamari da sunan ka ya fito."

"Saboda haka, muna gayyatar ka tattauna da mataimakin Sufeta Janar na Ƴan sanda, FCID Abuja a ranar Litinin 24 ga watan Agustan 2020 misalin ƙarfe 11 na safe a daki mai lamba 407, bene na uku a ginin FCID, Area 10 Garki Abuja."

Tsohon mataimakin gwamnan na CBN wanda ya yi digirinsa na uku a Jami'ar Oxford da ke Birtaniya ya ce wasu tsaffin mayaƙan Boko Haram ne suka faɗa masa amma daga baya ya sassauta abinda ya faɗi.

A halin yanzu dai Mailafia yana aiki ne a Cibiyar Nazarin Manufofi da Muhimman Buƙatu ta Ƙasa, NIPPS da ke Kuru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel