Juyin mulki a Mali: Zaman sulhu tsakan Soji da ECOWAS ya kare a baran-baran

Juyin mulki a Mali: Zaman sulhu tsakan Soji da ECOWAS ya kare a baran-baran

Zaman sulhun dake gudana tsakanin shugabannin kasashen yankin Afrika ta yamma ECOWAS da Sojojin kasar Mali ranar Litinin ya kare a baran-baran, PUNCH ta ruwaito daga AFP.

Bangarorin biyu sun zauna ne sakamakon juyin mulkin da ya faru makon da ya gabata.

A jawaban da bangarorin biyu suka saki, sun bayyana cewa shugaban kasan da aka kifar, Ibrahim Boubacar Keita, ya bayyana niyyar rashin son komawa kan mulki kamar yadda ECOWAS ta bukata da farko.

KARANTA WANNAN: Babban hadimin gwamna El-Rufa'i yayi mumunan hadarin mota a hanyar Abuja/Kaduna

Juyin mulki a Mali: Zaman sulhu tsakan Soji da ECOWAS ya kare a baran-baran
Juyin mulki a Mali: Zaman sulhu tsakan Soji da ECOWAS ya kare a baran-baran
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa Sojojin da su ka kifar da gwamnatin kasar Mali su na so su yi mulkin rikon kwarya na shekaru uku kafin shugabanci ya koma hannun farar hula a kasar.

Wata majiya daga tawagar shugabannin kasashen yammacin Afrika da ta gana da sojojin tawaye na kasar Mali ta bayyana wannan a ranar Lahadin da ta gabata.

“Sojojin tawaye sun tabbatar da cewa su na son su rike gwamnati na shekaru uku. Sojoji za su shugabanci wannan gwamnatin rikon kwarya da za a kafa.” Wani cikin 'yan tawagar Goodluck Jonathan da ta gana da ‘yan tawayen ya bayyanawa AFP haka.

Majiyar ta ce za a samu shugaban soji da zai rike gwamnati.

Haka zalika sojojin sun amince su fito da tsohon shugaba Ibrahim Keita, wanda aka tursasa ya yi murabus, tare da duk sauran shugabannin farar hula da ke tsare a Bamako.

“Kuma idan ya na so ya tafi kasar waje neman magani, wannan ba matsala ba ce.” Yace

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel