Dumu-dumu: Yadda aka kama matasa biyu suna luwadi da junansu

Dumu-dumu: Yadda aka kama matasa biyu suna luwadi da junansu

- Mazauna kauyen Agwete da ke birnin Kakamega na kasar Kenya sun lakadawa wasu matasa biyu mugun duka bayan sun kama su suna luwadi

- Kamar yadda jama'ar yankin suka tabbatar, Wayenso, daya daga cikin matasan, sun tabbatar da cewa ya saba lalata yaran jama'a

- Shugaban 'yan sandan yankin ya bayyana cewa, sun ceci matasan inda suka adana su a ofishinsu har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kan lamarin

Mazauna kauyen Agwete da ke garin Kakamega na kasar Kenya a ranar Juma'a da safe sun kama wasu matasa biyu a yayin da suke luwadi.

Shugaban kungiyar dattawan yankin mai suna Nyumbi Kumi, Reuben Otiende, ya bayyana cewa sun dade suna zargin daya daga cikin matasan mai suna Wanyeso Alias Gili, da zama dan luwadin.

An taba kama shi yayin da ya lalata wani yaron makwabcinsu, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Mazaunan yankin sun balle kofar Wanyeso bayan sun ga wani matashi wanda ba dan yankin ba mai suna Caleb Andani, ya shiga gidansa.

An kama matasan biyu dumu-dumu yayin da suke luwadin kuma jama'ar yankin sun lakada musu mugun duka kafin zuwan 'yan sanda.

K2TV ta ruwaito cewa, Wanyeso bazawari ne wanda ya saki matarsa mai suna Grace Khavesta a shekarar da ta gabata.

Allah ya albarkaci auren nasu da 'ya'ya uku kafin daga bisani su rabu.

Wani makabcinsa ya ce, "Wanyeso ya saki matarsa ne ta yadda zai ci karensa babu babbaka ta hanyar yin luwadin da ya saba."

Dumu-dumu: Yadda aka kama matasa biyu suna luwadi da junansu
Dumu-dumu: Yadda aka kama matasa biyu suna luwadi da junansu. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda jirginmu ya kusa ragargajewa a sararin samaniya - Aisha Buhari

Wani mazaunin yankin ya ce, "Muna kira ga mai gidan hayar da Wanyeso yake ciki da ya fattakesa saboda ba zamu ci da zama da dan luwadi a yankinmu ba. Wadannan ne mutanen da ke lalata mana yara."

Shugaban 'yan sandan Kakamega ta tsakiya, David Kabena, ya bayyana cewa wadanda ake zargin za a gurfanar da su bayan an kammala bincike.

Ba yau matsalar luwadi ke addabar al'umma ba. A kwanakin baya an kama wani mutum wanda ake zargi da lalata yara 12 a jihar Sokoto.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel