Alhamdulillah na samu lafiya, mun kusa hadari cikin hazo - Aisha Buhari ta yi maganarta na farko

Alhamdulillah na samu lafiya, mun kusa hadari cikin hazo - Aisha Buhari ta yi maganarta na farko

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, ta yi maganarta na farko bayan dawowa daga Dubai, hadaddiyar masarautar Larabawa UAE jinya.

Ta mika godiyarta ga yan Najeriya da suka sanyata cikin addu'o'insu yayinda take kwance babu lafiya a Dubai.

Ta ce yanzu ta warke kuma ta samu lafiya.

Aisha Buhari ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita da daren Asabar, 22 ga Agusta, 2020.

Yayinda dawowarta daga Dubai, Aisha ta bayyana cewa jirginsu ya dan samu mishkila cikin hazo amma matukan sun samu daman shawo kan lamarin.

Tace: "Ina son amfani da wannan dama wajen godewa yan Najeriya bisa addu'o'insu yayinda na tafi jinya. Yanzu na warke kuma na dawo gida, Najeriya."

"Yayinda muke hanyar dawowa, jirgin mayakan saman Najeriya ya samu matsala cikin hazo amma babban matukin jirgin da abokan aikinsa sun samu nasarar shawo kan lamarin."

"Ina jinjina da godiya kan matukan jirgin bisa namijin kokarin da sukayi."

A ranar 7 ga Agusta, mun kawo muku rahoton cewa an garzaya da uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, birnin Dubai, kasar UAE don jinyan ciwon wuyan da take fama da shi tun bayan zuwanta Legas, Daily Trust ta ruwaito.

An samu labarin cewa uwargidan shugaba Muhammadu Buhari ta tafi Dubai ne tun washe garin Sallah sakamakon ciwon wuya da take fama dashi bayan komawa birnin tarayya Abuja daga jihar Legas.

Yayinda ta koma Abuja, ta killace kanta na tsawon makonni biyu saboda ciwon wuyan da take fama da shi na kimanin wata daya bayan ta'aziyyar.

Abin ya tayar da hankalin na kusa da uwargidar kuma hakan ya sa aka garzaya da ita birnin Dubai don ganin Likita.

KU KARANTA: Bayan Jigawa, Bauchi, Yobe, Musulman Lauyoyin Kaduna sun yi hannun riga taron gangami saboda janye gayyatar El-Rufa'i

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel