Bayan Jigawa, Bauchi, Yobe, Musulman Lauyoyin Kaduna sun yi hannun riga taron gangami saboda janye gayyatar El-Rufa'i

Bayan Jigawa, Bauchi, Yobe, Musulman Lauyoyin Kaduna sun yi hannun riga taron gangami saboda janye gayyatar El-Rufa'i

Kungiyar Lauyoyi Musulamai a jihar Kaduna MULAN, ta sanar da janyewa daga taron gangamin Lauyoyin Najeriya da kungiyar lauyoyi NBA ta shirya sakamakon janye gayyatar da aka yiwa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

A taron hira da manema labarai a Kaduna ranar Asabar, shugaban kungiyar, Abbas Masanawa, ya bayyana cewa shawarar da uwar kungiya ta yanke kan janye gayyatar da tayi El-Rufa'i bisa wasu zarge-zarge maras tushe ba tare da kyautata masa zato ba nuna bangaranci ne na addini da kabila.

Musulman lauyoyin sun ce shin kungiyar NBA ta makance ne lokacin da ake yiwa mutane kisan kiyashi a jihohi irinsu Katsna, Zamfara, Neja da Birnin Gwari a Kaduna, amma sai yanzu idonsu ya bude da na kudancin Kaduna.

Kungiyar lauyoyin Musulman tace ta yaya za'a janye gayyatar El-Rufa'i amma a bar gwamnan Rivers, Nyesom Wike, wanda yayi ikirarin cewa jiharsa ta Kirista ce.

The Nation ta ruwaito shugaban Musulman Abbas Masanawa da cewa: "Dubi ga wannan shawara na takaici da uwar kungiyar NBA ta yanke, Kungiyar Lauyoyi Musulmai na jihar Kaduna basu da wani zabi face umurtan mambobinta da su janye daga halartan taron gangamin NBA kuma tana kira ga lauyoyi Musulami a Najeriya su bi sahu."

"Kungiyar Lauyoyi Musulmai na Kaduna na jaddada goyon bayansu ga gwamna Nasir El-Rufa'i a yunkurinsa na kawo karshen matsalar tsaro a jihar Kaduna , musamman kudancin Kaduna."

Bayan Jigawa, Bauchi, Yobe, Musulman Lauyoyin Kaduna sun yi hannun riga taron gangami saboda janye gayyatar El-Rufa'i
Bayan Jigawa, Bauchi, Yobe, Musulman Lauyoyin Kaduna sun yi hannun riga taron gangami saboda janye gayyatar El-Rufa'i
Asali: Facebook

Wannan ya biyo bayan janyewan kungiyar Lauyoyi a jihohin Jigawa, Bauchi da Yobe a ranar Juma'a, 21 ga Agusta, 2020.

Dukkansu sun bayyana cewa ba;a yiwa gwamna Nasir El-Rufa'i adalci ba kuma an nuna bagarancin addini. Saboda sun janye daga halartan taron gangamin da za'a yi a makon gobe.

A ranar Alhamis, Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta janye gayyatar da ta yi wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, zuwa wurin babban taronta bayan wasu daga cikin mambobin kungiyar sun nuna rashin amincewarsu.

NBA, wacce ta saka sunan El-Rufa'i a cikin manyan baki da za su gabatar jawabi a wurin taron, ta sanar da cewa ta janye gayyatar da ta yi masa a shafinta na Tuwita a ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Asali: Legit.ng

Online view pixel