Bayan gayyatar DSS, Rundunar Ƴan sanda ta gayyaci Mailafia zuwa Abuja

Bayan gayyatar DSS, Rundunar Ƴan sanda ta gayyaci Mailafia zuwa Abuja

Rundunar Ƴan sandan Najeriya ta gayyaci tsohon mataimakin shugaban gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Dr Obadiah Mailafia bisa wasu kalamai da ya furta yayin hira da aka yi da shi a gidan rediyo.

Ƴan sandan za su fara binciken su ne duk da cewa hukumar ƴan sandan farin kaya, DSS, tana gudanar da nata binciken a kan tsohon mataimakin gwamnan CBN ɗin.

Sai dai rundunar ta ƴan sanda ba ta ambaci dalilin gayyatar sa ba a cikin takardar da ta aike masa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Bayan gayyatar DSS, Ƴan Sanda sun gayyaci Mailafia zuwa Abuja
Bayan gayyatar DSS, Ƴan Sanda sun gayyaci Mailafia zuwa Abuja
Asali: UGC

Mataimakin kwamishinan ƴan sanda, Umar Sanda ne ya saka hannu a kan wasikar a madadin mataimakin Sufeta Janar na ƴan sanda, sashin masu binciken manyan laifuka, CID, da ke Abuja.

DUBA WANNAN: Za a aiƙe da Boubacar Keita zuwa Senegal - Soji

A takardar mai lamba 3000/X/FHQ/ABJ/VOI/245/8, mai ɗauke da kwanan wata 20 ga watan Agusta, ƴan sandan sun bukaci Mailafia ya zo ofishin hukumar sashin masu binciken manyan laifuka, Garki Area 10 Abuja a ranar Litinin 24 ga watan Agustan 2020 da karfe 11 na safe.

Takardar mai laƙabin "Ayyukan bincike, Binciken ƴan sana'a tana ɗauke sa gargadin cewa abin sirri ta ke ɗauke da shi kuma duk wanda ya fallasa abinda ta ke ɗauke da shi zai iya fuskantar hukunci."

Saƙon da ke jikin wasikar ya ce, "muna sanar da kai cewa wannan ofishin na bincike a kan wani lamari da sunan ka ya fito.

"Saboda haka, muna gayyatar ka tattauna da mataimakin Sufeta Janar na Ƴan sanda, FCID Abuja a ranar Litinin 24 ga watan Agustan 2020 misalin ƙarfe 11 na safe a daki mai lamba 407, bene na uku a ginin FCID, Area 10 Garki Abuja."

Tsohon mataimakin gwamnan na CBN wanda ya yi digirinsa na uku a Jami'ar Oxford da ke Birtaniya ya ce wasu tsaffin mayaƙan Boko Haram ne suka faɗa masa amma daga baya ya sassauta abinda ya faɗi.

A halin yanzu dai Mailafia yana aiki ne a Cibiyar Nazarin Manufofi da Muhimman Buƙatu ta Ƙasa, NIPPS da ke Kuru.

Da aka tuntube shi game da batun a wayar tarho a ranar Juma'a, Mailafia ya ƙi cewa majiyar Legit.ng komai inda ya ce su tuntubi lauyansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel