Anambra: Chris Ngige da APC su na tare da Gwamna Obiano a kan dakatar da Sarkin Alor

Anambra: Chris Ngige da APC su na tare da Gwamna Obiano a kan dakatar da Sarkin Alor

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa daya daga cikin manyan kasar Alor, a garin Idemili, jihar Anambra, ya yi na’am da dakatar da sarkinsu da aka yi.

Ministan kwadago da samar da aikin yi, Sanata Chris Ngige ya nuna goyon bayansa ga gwamnati na cirewa Sarki Elibe Mac-Anthony Chinedu Okonkwo rawani.

Mai martaba Igwe Elibe Mac-Anthony Chinedu Okonkwo ya na cikin sarakunan da gwamnan jihar Anambra ya dakatar saboda zun ziyarci shugaban kasa ba bisa ka'ida ba.

Wadannan sarakuna na gargajiya 13 sun je wurin shugaba Muhammadu Buhari ne a fadar shugaban kasa ba tare da umarnin mai girma gwamnan jihar Anambra ba.

Da ya ke magana da ‘yan jarida, Chris Ngige ya ce tun farko mutanen garin Alor ba su goyon bayan kakaba masu su Mai martaba Mac-Anthony Chinedu Okonkwo da aka yi.

A cewar ministan, Peter Obi ne ya fara nada Igwe Mac-Anthony Chinedu Okonkwo a matsayin Sarkin kasar Alor, shi kuma Willie Obiano ya tafi da shi bayan ya zama gwamna.

Ngige ya nuna ya yi maraba da wannan mataki da gwamnatin Willie Obiano ta dauka a kan Mac-Anthony Chinedu Okonkwo, duk da cewa su na da banbancin ra’ayin siyasa.

KU KARANTA: 2023: Gwamnan Ekiti ya ba Masoya kunya, ya ce a daina yi masa kamfe

Anambra: Chris Ngige ya na tare da Gwamna Obiano a kan dakatar da Sarkin Alor
Ngige ya goyi bayan dakatar da Sarki a Anambra
Asali: Facebook

Ministan ya ke cewa kafin yanzu majalisar mutanen Alor watau APC, ba ta tare da Mai martaba Mac-Anthony Chinedu Okonkwo, saboda ba a son ransu ya hau kujera ba.

A wani jawabi da shugaban APC, Uzoma Igbonwa ya fitar a madadin mutanen Alor, ya yi Allah-wadai da sabawa gwamnatin jihar Anambra da sarki Igwe Chinedu Okonkwo ya yi.

A wannan jawabi da kungiyar ta fitar, ta ce ta na goyon bayan gwamnatin jiha, kuma ta goyi bayan dakatarwar da aka yi wa Sarkin Alor domin a dawo da kimar sarakuna.

“Mu na jaddada cikakkiyar goyon bayanmu ga gwamna a kan matakan da ya dauka na dawowa sarakunan gargajiya da martabarsu ta dakatar da sarakuna har da na kasar Alor.”

“Mu mutanen Alor mu na da son zaman lafiya da bin doka, mu na tare da gwamnan Anambra, kuma za mu cigaba da yi masa biyayya. Ba mu tare da aikin Mac-Anthony Chinedu Okonkwo.”

Kungiyar ta yabawa Chris Ngige, ta kuma roki ministan ya yi amfani da ofishinsa, ya roka masu shugaban kasa a ba su damar nada mutumin da su ke so a matsayin sarkinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel