An kama bakin haure guda 3 da suke shigowa da 'yan ta'addar Najeriya makamai

An kama bakin haure guda 3 da suke shigowa da 'yan ta'addar Najeriya makamai

- Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar cafke wasu mutane uku da suka shigo Najeriya daga kasashen dake makwabtaka

- Bakin hauren dai ana zarginsu da shigowa da 'yan ta'addar dake yankin Arewa maso Yamma makamai

- An cafke su dauke da makamai da harsashi masu yawan gaske

Wasu bakin haure guda uku da suke shigowa da 'yan ta'addar dake yankin Arewa maso Yamma makamai sun shiga hannu, bayan jami'an hukumar soji dake kula da hiyyar jihar Sokoto sun cafke su.

Mai magana da yawun helkwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar John Enenche, yace masu laifin wadanda suka yi shiga irinta 'yan Najeriya an kama su da makamai a kauyen Dantudu dake Mailailai cikin karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sokoto.

An kama bakin haure guda 3 da suke shigowa da 'yan ta'addar Najeriya makamai
An kama bakin haure guda 3 da suke shigowa da 'yan ta'addar Najeriya makamai
Asali: Facebook

Makaman da aka samu a wajensu sun hada da bindiga mai kirar AK-47 guda shida, harsashi guda 2,415, inda duka aka samo su a cikin abubuwan hawan da suke amfani da su wajen tafiye-tafiyensu.

KU KARANTA: An kama likitan bogi da yake bawa mutane maganin coronavirus a Najeriya

An kuma gano cewa wadanda ake zargin suna hannun jami'an tsaron ana cigaba da gabatar da bincike akansu, inda daga baya za a mika su ga hukumar da ta dace domin yi musu hukunci.

Enenche ya kara da cewa:

"Hakan na nuni da cewa wasu matsalolin tsaron dake faruwa a Najeriya akwai sa hannun mutanen da ba 'yan kasar ba. Wadanda ake zargin yanzu suna hannu ana cigaba da gabatar da bincike akan su kafin a danka su a hannun hukumar da ta dace domin gabatar da hukunci a kansu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel