Wani mutumi ya biya N220,000 kudin asibitin mai jegon da aka tsare makonni biyu bayan haihuwa

Wani mutumi ya biya N220,000 kudin asibitin mai jegon da aka tsare makonni biyu bayan haihuwa

An tsare Halima da sabon jaririnta a asibiti tsawon makonni biyu sakamakon gaza biyan kudin aikin tiyatan da akayi mata, N220, 000.

Bayan rahoton da Vanguard tayi makon da ya gabata, wani mutumin arziki ya biya kudin asibitin kuma an sallameta.

Vanguard ta samu rahoto daga wata kungiyar kare hakkin yara cewa saurayin Halima ya yi watsi da ita bayan ta samu juna biyu kuma an tsareta a asibiti bayan haihuwa.

Bayan biyan kudin da mutumin arzikin yayi, manema labarai sun ziyarci sabon jaririn a unguwar Mushin dake jihar Legas inda suke zama.

Daga ganin irin muhallin da Halima ke zama, za ka fahimci cewa tana bukatar taimako.

KUU KARANTA: Soji sun kashe yan Boko Haram 8, an yi rashin jaruman Soji 3 a garin Kukawa

Wani mutumi ya biya N220,000 kudin asibitin mai jegon da aka tsere makonni biyu bayan haihuwa
Wani mutumi ya biya N220,000 kudin asibitin mai jegon da aka tsere makonni biyu bayan haihuwa
Asali: Facebook

A cewarta, saurayinta ya ki amincewa da juna biyun da ta samu kuma ya umurceta ta zubar da cikin ko su rabu.

"Na yi iyakan kokarin ganin na zubar da ciki amma abin ya ci tura, amma lokacin da yace inje a zubar min a asibiti ta hanyar tiyata, naki amincewa saboda ina tsoron rasa raina, shi yasa nayanke shawarar ajiye cikin." Tace

"Na sha bakar wahala lokacin da nike dauke da cikin kuma rokon abinci nike daga wurin mutane. Sau da dama makwabcina, limamin Masallacinmu, ke taimaka min da kudin abinci har zuwa lokacin da na daina iya tambayansa saboda na zaman masa nauyi."

"Shine wanda ya bayyanawa mutane labari na saboda in samu taimako."

"Ina matukar godiya ga mutumin da ya biya kudin asibitina."

Halima tana mai kira ga yan Najeriya su taimaka mata a wannan lokaci saboda tana bukatan ciyar da jaririnta da kuma muhalli mai kyau.

Ga masu niyyar taimako, Halima na zaune a:

No 54, Post Office Road, Muslim, Lagos

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel