NDLEA ta kama manyan kwantena shaƙe da ƙwayar Tramadol a Legas

NDLEA ta kama manyan kwantena shaƙe da ƙwayar Tramadol a Legas

Hukumar Yaki da Safarar Miyagun Kwayoyi ta NDLEA ta gano wani kwantena mai tsawon sahu arba'in shake da kwayar Tramadol da wasu haramtattun magunguna a tashar Brawal da ke Legas.

Mai magana da yawun hukumar Mr Jonah Achema ne ya sanar da hakan a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewar sanarwar, Shugaban NDLEA, Kwanel Muhammad Abdullah (mai murabus) ya ce an gano wannan bayan da yan sanda suka kama wata kwantena mai tsawon kamu arbain shake da buroshi da katon din Tramadol 40 da wasu haramtattun kwayoyin.

NDLEA ta kama babbar kwantena shake da kwayar Tramadol
NDLEA ta kama babbar kwantena shake da kwayar Tramadol. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An nadi bidiyon ‘Yaran Magu’ suna neman toshiyar bakin N75m daga hannun ɗan kasuwa

"Idan za ku iya tunawa yan sandan Apapa a Legas sun kama wata kwantena mai tsawon kafa 40 shake da kwayoyi da ake zargin Tramadol ne da Kodin a ranar 6 a watan Agusta.

"An kama wannan kwantenar ne a ruwa sannan aka dauke ta aka kai tashar Apapa.

"Binciken da NDLEA ta gudanar ya yi sanadin gano wani kwantana mai kafa 40. Binciken hadin gwiwa da aka yi ya nuna akwai katon 255 na Tramadol daban daban da wasu haramtattun kwayoyin.

"Binciken ya nuna cewa wannan Tramadol din a kasar akistan aka kera su, hakan sabon lamari ne domin wadanda aka kama a baya a India aka kera su.

"Wannan lamari ne da duniya ke saka ido a kai. Safarar miyagun kwayoyi na daya daga cikin manyan abin da ke asassa rashin tsaro a yankunan kasar nan.

"Abdullah ya ce wannan babban nasara ce ga binciken da hukumar ke yi domin an gano sabuwar hanyar da ake shigo da miyagun kwayoyi daga Pakistan zuwa Turai kafin ya shigo Najeriya.

"An boye kwayoyin Tramadol din ne a cikin kwalayen buroshi.

"Abdullahi ya ce zai cigaba da bincike har sai ya gano ainihin wadanda suke shigo da kwayoyin kuma ya yi kira ga sauran hukumomin tsaro su hada kai da NDLEA wurin saman nasarar binciken.

"Ya yaba da kokarin rundunar yan sanda, NAFDAC da sauran hukumomi da ke basu hadin kai wurin binciken," a cewar sanarwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel