Kano: Matashi ya kashe abokinsa kan N500

Kano: Matashi ya kashe abokinsa kan N500

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Sani Ibrahim mai shekaru 22 a duniya wanda aka zargi wani abokinsa da halaka shi saboda rashin jituwa da ya shiga tsakaninsu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Habu Sani, ya bayyana cewa wanda ake zargi da aikata kisan ya yi hakan ne a kan naira 500, inda ya caka masa wuka a kirji wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

Wani da abun ya faru a idonsa mai suna Basiru Ahmad, ya ce yan mintoci kafin faruwar lamarin, matasan biyu sun tsaya a wurinsa har ma ya yi masu nasiha a kan zama lafiya da junansu sannan suka tafi.

"Sun zo wajena mintina kaɗan kafin faruwar al'amarin, don mun gaisa da su har na yi musu fada cewa su zauna lafiya, babu hayaniya suke cewa da ni ai babu komai.

''Daga nan sai shi Sani Ibrahim ya je fitsari, to da yake gurin da duhu ban iya gane waye ya je inda yake fitsarin yake masa magana ba, sai na ga wani ma ya je kansa, daga nan sai jin kararsa muka yi su kuma wadancan sun gudu'', a cewar Basiru Ahmad.

Kano: Matashi ya kashe abokinsa kan N500
Kano: Matashi ya kashe abokinsa kan N500 Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Wani daga cikin abokan mamacin Sani Alhassan ya ce suna gefe suna hira bayan dawowarsa daga sana'arsa ta tuka a-dai-dai-ta sahu.

Sai suka ga ana taruwa a inda aka kashe matashin, shi ne suka je suka tarar da Sani a kwance ya dafe kirjinsa, yana ambatan sunan wanda ake zargi da kashe shi.

Mahaifiyar marigayin mai Zainab Isma'il a hirarta da BBC ta nemi hukuma da ta bi mata hakkin danta, wanda ta ce maraya ne kuma shi ke daukar nauyin ita.

Ta ce: ''Gani na da shi na karshe shi ne lokacin da ya shigo don ya gaishe ni saboda ba ni da lafiya, daga nan sai ya ce tun da bacci nake bari ya je ya dawo.

''Can kuma sai na ji ana sallama ana cewa wai in zo ga Sani can an caka masa wuka a kirji, shi ne na ce ba zan je ba su kawo min shi kawai don duk kirji makasa ne, kashe shi dama suka yi niyar yi."

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin kano ta bada hutun sabuwar shekarar musulunci

Mahaifiyar mamacin ta ci ga da cewa: ''Shi kadai nake da shi kuma shi ke taimaka min, ya kan je Fatakwal yana harkar gwangwan dinsa, kuma da tuni ya tafi amma saboda rashin lafiyar da nake shi ya sa bai tafi ba ya ce sai na ji sauki.

"Dama suna yawan tsokanar sa, amma duk da na hana shi daka ta tasu su yi fada amma sai sun takale shi."

A halin da ake ciki, kwamsihinan 'yan sandan jihar ya tabbatar da kama wanda ake zargin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

An kuma mika batun zuwa ga sashen binciken manyan laifuka na rundunar yan sandan jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel