Da duminsa: Majalisar dinkin duniya za tayi ganawar gaggawa gobe kan lamarin juyin mulki a Mali

Da duminsa: Majalisar dinkin duniya za tayi ganawar gaggawa gobe kan lamarin juyin mulki a Mali

Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya za tayi ganawar gaggawa kan lamarin kasar Mali ranar Laraba, kwana daya bayan juyin mulki Sojoji a kasar yamacin Afrikan.

Kasar Faransa da Nijar ne suka bukaci a yi ganawar kuma za ta gudana a sirrance ranar Laraba, wani babban jami'in MDD da ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa AFP

Hakazalika, sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya yi Alla-wadai da damke shugaban kasar Mali kuma ya bukaci "a sakeshi ba tare da bata lokaci ba".

"Sakatare Janar ya yi tirr da wannan abu kuma ya yi kira da mayar da halastaccen shugabanci da doka a Mali," mai magana da yawun Guterres ya bayanna

Da duminsa: Majalisar dinkin duniya za tayi ganawar gaggawa gobe kan lamarin juyin mulki a Mali
Antonio Gutrres
Asali: Facebook

A bangare guda, Gamayyar kasashen nahiyar Afrika AU, ta yi Alla-wadai da damke shugaban kasan Mali, Ibrahim Keita da Firam Mininsta Boubou Cisse, da sojojin kasar sukayi

Legit ta kawo muku rahoto cewa wasu Sojoji a MaLi yau Talata sun damke shugaban kasa da wasu mamabobin majalisarsa a gidansa dake BamakO, babbar birnin kasar.

"Muna masu fada muku cewa shugaban kasa da Firam Minista na hannunmu" Daya daga cikin Sojin ya bayyanawa AFP.

Martani kan hakan, shugaban gamayyar kasashen Amfirka, Mousa Faki, ya yi kira ga sakin su biyu ba tare da bata lokaci ba.

Hakazalika ya yi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin duniya su nuna rashin amincewarsaru da yunkurin amfani da karfin Soja wajen mulki a Mali.

Faki ya bayyana hakan ne a shafin na Tuwita.

Gabanin damke shugaban kasan a yau Talata, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, wanda shine wakilin ECOWAS da aka tura sulhunta rikicin Mali, ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari.

Ya bayyanawa Buhari cewa kungiyar adawa a kasar Mali, M5, ta doge kan bakanta cewa sai shugaba Keita ya yi murabus

Za ku tuna cewa a watan Yuli, shugaba Buhari da wasu shugabannin ECOWAS sun kai ziyara kasar Mali domin sulhunta bangarori biyu amma ganawarsu da shugaban hamayya, Imam Dicko, ya kare a baran-baran.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel